Yanzu-Yanzu: Yahaya Malumfashi, Yakubu Kafi Gwamna na shirin Kwana Casa’in ya rasu – Hausa Daily Times


Rahotannin da ke fitowa daga masana’antar Kannywood sun tabbatar da rasuwar Alhaji Yahaya Umar Malumfashi wanda aka fi sani da Yakubu Kafi Gwamna na cikin shirin Kwana Casa’in.

Hausa Daily Times ruwaito mamacin ya yi fama da jinya na tsawo watanni inda a makon jiya ya nemi adu’a daga Al’ummar musulmi dangane da halin rashin lafiya da yake ciki.

Fitaccen marubuci a masana’antar kuma dan jarida Nasir S. Gwagwazo ya tabbatar da mutuwar a shafin sa na Facebook.

Ya ce” Inna lillahi wa inna ilaihir raji’in! Allah ya gafarta maka, Ya sa mutuwa hutu ce a gare ka, Marigayi Umar Yahaya Malumfashi!
#RIP”.

Karin bayani na tafeee.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts