‘Yan-sane sun sace wayar tsohon mataimakin Shugaban kasa – Hausa Daily Times


Wasu ‘yan-sane sun sace wayar tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, a dakin taro na NA Centre, da ke Abuja.

An gayyaci tsohon mataimakin Shugaban kasan ne a matsayin babban baƙo a wurin gabatar da littafin tarihin rayuwa tare da ƙaddamar da Cibiyar Jagorancin Solomon Lar, tsohon Gwamnan jihar Lagos kuma shugaban jam’iyyar PDP na farko.

Labarin satar ya fito ne daga daya daga cikin wadanda aka gayyata, Shehu Sani, a shafin sa na Twitter.

“Abin mamaki ne cewa wani zai iya keta tsauraran matakan tsaro ya sace wayar tsohon VP Sambo a wajen kaddamar da littafin tarihin rayuwar Marigayi Solomon Lar a Abuja,” Sanata Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts