Yajin aikin ASUU yana matukar min ciwo – Buhari – Hausa Daily Times


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin kira ga kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin da su koma ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar karancin kayan aiki.

Shugaban, wanda ya sake nanata kiran a wani jawabi da ya yi a fadin kasar a ranar Asabar a Abuja, ya ce ya ji takaicin yadda ake ci gaba da tabarbare harkokin ilimin manyan makarantun kasar nan.

Wannan jwabin wani bangare ne na bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba nemo kudade a Najeriya da ma kasashen duniya, wajen samar da tallafin ilimi domin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ingantaccen ilimi da kwarewa a sana’o’i daban-daban.

“Dole ne in furta cewa ina jin zafi sosai game da tabarbarewar da tsarin ilimi ke kara yi a manyan makarantumu.

“Ina amfani da wannan bukin ranar samun ‘yancin kai ne domin nanata kirana ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aiki da su dawo ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar karancin kayan aiki”.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts