Yajin Aiki: “Ina da kwarin gwuiwa kan matakin da Buhari zai dauka kan ASUU” Gbajabiamila – Hausa Daily Times


Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya bayyana amincewarsa game da yadda ake sasanta rikici tsakanin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin tarayya.

Gbajabiamila, wanda ya yi magana a ranar Juma’a a fadar shugaban kasa bayan wani zama da shugabannin majalisar suka gudanar da shugaban kasa, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba shugaban kasa zai bayyana sakamakon ganawar.

Idan dai ba a manta ba a ranar Talata ne shugabannin majalisar suka gabatar da rahoto mai kunshe da shawarwari biyo bayan ganawar da suka yi da masu ruwa da tsaki a rikicin ASUU da gwamnati da shugaban kasa ke ci gaba da yi bayan an shirya gudanar da taron na gaba a ranar Alhamis.

Da yake lura da cewa nan ba da dadewa ba za a iya ganin karshen rikicin, Gbajabiamila ya ce zama na da kyau domin za a kawo karshen matsalar.

Ya ce: “Mun zo nan ne don bin diddigi, wanda ya kamata mu zo jiya amma Shugaban kasa ba ya nan, kuma wannan bibiya ce.

“Mun sake tattaunawa mai ma’ana sosai tare da shugaban kasa kan batutuwan da ke kasa kuma za a kammala wannan batu, kai tsaye za ku ji ta bakin shugaban, amma ya kamata mu bayyana cewa ganawar tamu a yau ta yi kyau matuka.

“Tabbacin shine cewa mun gana da shugaban kasa, mun tattauna, ganawar ce mai kyau kuma ko shi shugaban ya bayyana cewa ya ji dadi ganawar sossai”.

Shugaban Majalisar ya ce bana son ya yi riga Malam masallaci, ya bukaci ‘yan Najeriya da su jira ganin irin matakin da shugaban kasa zai dauka kan batutuwan da ke gabansa.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts