Wani ɗan Najeriya ya bayyana yadda ya yi nasara da ya je wurin jarabawar neman aiki (interview) a wani katafaren Kamfanin a ƙasar Burtaniya.
Matashin mai suna Toyyib Adewale, jaridar Legit ta ruwaito Hausa Daily Times ta fassara cewa, ko da masu gudanar da jarabawar kamfanin suka tambaye shi yadda zai iya gudanar da aiki a kamfanin cikin matsi, sai ya amsa da cewa:
- Yadda wani ɗan talakan Najeriya ya samu aiki a wani katafaren kamfani a London
- ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni huɗu
“Ni ne ɗa na farko a gidan mu. Na yi karatu a makarantar firamaren da iyayena ba su iya biya kuɗin makaranta na don haka sai na ɗaya na ke zuwa a aji a kowane zangon karatu domin ta haka ne zan iya ci gaba da karatu a makarantar ƙarƙashin tallafin karatu da ake bai wa duk wanda ya zo na ɗaya domin yin karatu kyauta (scholarship). Sannan ana amfani da littattafai na ne wajen koyar da ‘yan uwana a gida. … Don haka ba zan iya bari na zo na biyu ba a ajin mu sabida wannan dalilin.”
Toyyip, ya ce kafin ya bar harabar kamfanin, an ɗauke shi aiki.
Toyyib ya ce “Ka tuna da ba da labarinka.”
Related