Yadda maharba suka kubutar da sama da mutum 20 daga yan bindiga a Neja


Maharba da aka fi sani da yan Sa Kai ko (Special Hunters) a jihar Neja sun kubutar da mutane sama da 20 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Kuchi da ke a karamar hukumar Munya.

Yan ta’addan sun afka wa garin Kuchi da ke da nisan kasa da kilomita 7 da shalkwatar karamar hukumar ta Munya, wato Sarkin Pawa da misalin karfe 2 na tsakar daren Alhamis, inda suka rika bin gida-gida suna kama mutane kafin daga bisani su tasa keyarsu zuwa maboyar su.

Guda daga cikin wadanda aka kubutar din da ya bayyana sunan sa da Muhammad Auwal, ya ce yan Special Hunters sun yi namijin kokari wurin kubutar da su, sannan sun kashe da dama daga yan ta’addan kuma babu ko daya daga cikin su da yan ta’addan suka kashe ko raunata.

Ya kuma ce yan kungiyar sa kan sun yi nasarar kubutar da su ne a lokacin da yan ta’addan suka gagara tsallakawa da su wani rafi wanda ya kawo ruwa sossai sanadiyyar ruwan sama mai karfi da aka kwana ana yi a wannan rana.
Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts