Mutum daya ya nutse, wani kuma ya samu rauni a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Nansa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Alhaji Ahmed Inga, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA) ne ya bayyana hakan a zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar a Minna.
- Buhari bai san ma an yi barazanar kama shi ba sai da na fada masa- Gwamna El-Rufa’i
- Naira ta yi mugun faduwa a kasuwar bayan fage, ta kai $1/N710
Ya bayyana cewa hukumar a jiya Asabar ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da wasu fasinjoji da suka dauko kaya daga kauyen Nansa.
Inga ya ce kwale-kwalen na kan hanyar zuwa kasuwar Zumba da ke ci duk ranar Asabar, inda ya yi karo da kututturen bishiya ya rabe biyu a tsakiyar kogin.
Ya ce mutum daya ne ya nutse yayin da daya kuma ya samu rauni, ya kara da cewa aikin ceton na tafiyar hawainiya domin yankin da lamarin ya faru ya kasance mabubayar ‘yan ta’adda saboda masu aikin ceto na fargabar a yi garkuwa da su.
Related