Wani gini ya rufta a Kano, ya kashe ‘yan gida daya – Hausa Daily Times


Wani bene mai hawa daya ya ruguje a ranar Juma’a a cikin birnin Kano, inda ya kashe ‘yan gida daua su biyu ‘yan shekara 15 da 11.

Sai dai, an ceto babban yayansu mai shekaru 17 da rai.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya bayyana haka a ranar Asabar a Kano, inda ya ce gidan na unguwar Kofar Mata Hauren Gadagi a Kano.

“Mun sami kiran waya da misalin karfe 10:50 na dare daga wani Jamilu Salisu-Zango cewa ginin gida bene mai tsawon kafa 50 x 40 ya ruguzo.

Mun aika da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru kuma an fito da ’yan’uwan uku ginin ya rufto a kan su. Biyu daga cikinsu ba su cikin hayyacinsu ,” in ji shi.

Mista Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin Murtala domin ceto rayuwarsu inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ​​biyu daga cikin su.

Ya ce an mika gawarwakin ga ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Kofar Wambai, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts