Tun da aka yanke ƙafar fatima mun so mu yi sulhu da iyayen fatima, amma… Mahaifiyar Aliyu


Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sakkwato

Wata ɗaya da samun rahoton yanke ƙafar wata ɗaliba mai suna Fatima a lokacin da take murnar kammala jarabawar NECO ga ɗaliban makarantar sakandiren Kalifa da ke Sakkwato wacce ake kira Khalifa International Secondary School, har kawo yanzu ana cigaba da taƙaddama tsakanin dangin Fatima da dangin Aliyu, wanda ya yi sanadiyyar buge Fatima har sai da aka yanke ƙafarta.

A wani sautin murya da ke nuni da mahaifiyar Fatima ce Hajiya Hadiza, an ji tana ta bayyana cewa babu maganar yafiya tsakanin su da Aliyu, koda sama da ƙasa za su haɗe, har sai an biya su diyyar ƙafar ýar su Fatima.

A wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a Sakkwato, Mai Bai wa Gwamna Shawara a kan Haƙƙokin Bil’Adama Hajiya Ubaida Bello, ta bayyana cewa sun yi zaman sulhu da iyayen Fatima, Iyayen Aliyu da Jami’ai na Hukumar Kare Haƙƙokin Ɗan Adam, sai dai an tashi babu daɗin rai, domin mahaifin Fatima ya yi wasu maganganu marasa dadi da ke nuna da cewa shi ba zai sulhunta da kowa ba, sai dai a biya shi diyyar kafar ‘yar shi da kuma diyyar ɓacin ran ta na har iyakar rayuwar ta.

Ta ƙara da cewa, “A lokacin da muka yi zama da mahaifiyar yaron tare da manema labarai, ta shaida mana cewa sun bi duk hanyar da za a bi wurin ganin an samu sulhu tsakanin mu da dangin Fatima tun farkon lokacin da abin ya faru har zuwa yanzu, amma dangin Fatima ba su aminta an yi sulhu ba.”

A cewar ta, “Mun ba da duk abin da ake buƙata ga lafiyar Fatima ba tare da kasawa ko gajiyawa ba, amma iyayenta basu haƙura ba. Mun shaida musu mun ɗauki nauyin komai na jinyarta har zuwa samun sauƙi da yi mata ƙafar roba, amma basu haƙura ba.”

“A duk Lokacin da na je asibiti domin duba Fatima hantarata atke yi. Na rasa barci da cin abinci saboda yanayin Fatima, ” in ji Mahaifiyar Aliyu.

Duk da dagewar da iyayen Fatima suka yi na ganin an ladabtar da ɗanta Aliyu, mahaifiyar sa na ganin samun haɗin kan iyayen Fatima na da matuƙar muhimmanci, don kula da lafiyar yarinyar da makomar rayuwar ta, shi ya fi kamata a mayar da hankali a kai. Ba suna matsawa a sasanta don kawai jin daɗin ɗan su kaɗai ba ne.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts