Taron ƙungiyar FOMWAN na ƙasa karo na 37 ya yi armashi


Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal

Mai Alfarma, Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar CFR mni, Shugaban majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Kasa, ya halarci bukin buɗe taron shekara shekara na ƙasa na Kungiyar Tarayyar mata Musulmi ta kasa, FOMWAN karo na 37 a garin Fatakwal, na Jihar Ribas, wanda aka fara tun a 8 zuwa 11 ga watan Satumba 2022.

Mai Alfarma, Sarkin Musulmi a duk shekara yana halartar taron kungiyar, kamar na sauran manyan ƙungiyoyin Musulunci masu da ke ƙarƙashin jagorancin Jama’atu Nasril Islam, irin su MSSN, NACOMYO da sauran su.

Kafin soma taron, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya kai wa Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ziyara kamar yadda yake bisa al’ada, don girmamawa.

Sarkin Musulmi na tare ne da rakiyar wasu daga cikin ‘yan majalisar sa tare da shugabanni da mambobin ƙungiyar FOMWAN.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts