Ta Tabbata: Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabuwar kungiyar ASUU – Hausa Daily Times


Ministan kwadago da samar da aikin yi, Chris Ngige ya gabatar da takardar shaida ga kungiyar ma’aikatan koyarwa na jami’o’in Najeriya, wadda ta kasance kungiya ta malaman jami’o’in tarayya da na jihohi.

Kungiyar mai suna CONUA a takaice ana ganin kai tsaye za ta kasance kishiya ga babbar kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU.

Wani jami’in gwamnatin Najeriya ya wallafa cewa an kafa kungiyar CONUA ne a shekara ta 2018 a jami’ar jihar Osun, a cewar BBC.

Kungiyar ASUU da gwamnatin Najeriya na ci gaba da dambarwa saboda yajin aikin sai-baba-ta-gani da malaman jami’o’in suka shiga tsawon wata takwas ke nan yanzu, suna neman sai lallai gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Baya ga kungiyar CONUA, ministan kwadagon ya kuma amince da kungiyar likitoci masu koyarwa ta kasa (NAMDA)

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts