Sojoji sun dakile yunkurin yan ta’adda na kai hari makarantar horar da lauyoyi a Abuja


Kimanin sa’o’i 24 da ‘yan ta’adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a wani faifan bidiyo, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa sojojin Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da sojojin, Jaridar The Nation ta ruwaito.

Akwai rahotannin sirri, kamar yadda majiyar sojoji ta bayyana, ‘yan ta’addan sun mamaye babban birnin tarayya Abuja da nufin kai hari a makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati.

Majiyoyin soji da suka nemi a sakaya sunansu sun ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin amma hukumomi sun ce suna nan suna bin maharan.

A cewar daya daga cikin majiyoyin, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi wa dakarun 7 Guards Battalion da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna.

Ya kara da cewa sojoji uku ne suka jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibitin domin kula da lafiyarsu.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Harin kwanton bauna da ya faru a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna cikin kusa da wurin kuma maiyuwa ne su aiwatar da shirinsu na kai farmaki a makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya.

Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Brigade, Kyaftin Godfrey Abakpa, ya tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai wa sojoji hari amma an samu nasarar dakile su.

Ya kara da cewa an kwashe sojojin da suka samu raunuka zuwa asibiti kuma suna samun kulawa.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts