Shugaba Buhari ya yi fama da matsalar zautuwa tsawon shekaru – Aisha Buhari – Hausa Daily Times


Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shafe shekaru da dama yana fama da matsalar zautuwa ta (PTSD) bisa shigarsa yakin basasar Najeriya da hambarar da gwamnatinsa ta mulkin soja da aka yi tare da tsare shi na tsawon watanni 40 ba tare da aikata laifin komai ba.

Uwargidan shugaban Najeriya, yayin da take bayyana hakan a ranar Talata a wurin bikin kaddamar da cibiyar kula da masu matsalar zautuwa ta rundunar sojojin Najeriya (AFPTSDC) ta ce rashin nasarar da Buhari ya yi na zabuka uku a jere ya kara dagula lamarin.

Ta bayyana cewa, koda aka aura mata Shugaba Buhari a gidansa ta cika shekara 19, ta bayyana cewa ta sha fama da matsalar ta shugaban kasa tun a farkon aurenta.

Uwargidan shugaban ta ce, “Hakika dole sojoji da iyalan su kasance da juna, duk da mummunan sakamakon da suke samu. Kasancewa matar tsohon soja kuma ƙwararriya a fannin lafiya, na fahimci ƙalubalen da ke tattare da matsalar zautuwa ta PTSD da tasirinta ga iyalan soja da ma ƙasa.

“Mijina ya yi aikin sojan Najeriya na tsawon shekaru 27 kafin a yi masa juyin mulki. Ya yi yakin basasa na tsawon watanni 30 ba tare da samun kulawar kwararrun lafiya ba; ya shafe watanni 20 yana mulkin Najeriya kuma an tsare shi tsawon watanni 40 ba tare da bayyana irin laifin da ya aikata ba.

“Bayan shekara daya da fitowa daga kurkuku, muka yi aure. Na sha wahala sossai sakamakon matsalar nan, saboda na fuskanci waɗannan abubuwan, yayin da nake da shekaru 19. Ba abu mai sauki bane  kula mai irin wannan matsalar da ya kasance tsohon shugaban kasa kuma babban kwamandan sojojin Najeriya, fada ma irin wadanda ke cikin wannan hali sun yi kuskure zai kasance babban kuskuren da za ku yi.

“Saboda haka, ina ‘yar shekara 19, dole na gano yadda zan gaya wa mai irin darajarsa cewa ya yi kuskure ko daidai kuma hakan ne farkon laifina a gidansa, da kuma tsayawarsa takara a shekarar 2003, 2007 da 2011 kuma duka ya fadi, duk cikin irin wannan yanayi ba tare da samu taimakon kwararru ba, dole na zama kwararriya a bangaren lafiyar kwakwalwa.”

Ta yaba da sadaukarwar da jami’an soji suka bayar da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen gina kasa, inda ta ce, “da wwnnan, ina so in yi amfani da wannan dama domin in yaba wa sojojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke bayarwa wajen gina kasa.

“Dakarun da suka mutu za su ci gaba da zama abin tunawa a zukatan mu. Ina yaba wa mata da iyalansu; kuma ina so in sanar da su cewa duk al’ummar kasar na tare da su.”

A’isha ta bayyana cewa cibiyar PTSD da ta kaddamar yana da muhimmanci ga jami’an soji da ma sauran su, inda ta jaddada cewa sojoji ne farkon wadanda abin ya shafa.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts