Sanatocin PDP na barazanar tsige Buhari in bai magance matsalar tsaro ba


Mambobin jam’iyyar PDP a majalisar dattawan Najeriya sun ba wa shugaba Buhari wa’adin makonni shida da ya magance tabarbarewar tsaro a fadin kasar ko kuma a tsige shi.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Phillip Aduda, ya bayyana matsayin ‘yan majalisar a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a zauren majalisar a Abuja.

Sanatocin PDP sun gudanar da zanga-zangar ne bayan da shugaban majalisar ya ki barin Aduda ya yi magana. Sanata Aduda ya gabatar da wani batu inda ya nemi shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da ya tattauna batun tsaro a kasar nan da kuma batun tsige shugaba Buhari. Sai dai shugaban majalisar dattijai wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ki amincewa da bukatar shugaban marasa rinjayen.

Sanatocin jam’iyyar adawar dai ficewa suka yi daga zauren majalisar ba tare da jiran kammaluwar zaman na yau Laraba ba.
Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts