Sakon gaggawa daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi


Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta ƙasa wato JNI, ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na lll CFR, MNI, na kira da jan hankali ga waɗanda har yanzu ke jinkiri wajen yin rijistar katin zaɓe, da kuma matasa da suka kai munzalin mallakar katin zaɓe, da a hanzarta yin rijista kafin cikar wa’adin da hukumar INEC ta keɓe na yin rijistar masu kaɗa kuri’a.

A guji yin rijista fiye da sau ɗaya, don yin hakan ya saɓawa ƙa’ida ta yin cikakken zaɓe a lokacin zaɓuɓɓukan ƙasa da ke tafe. Ga waɗanda sun yi rijista amma ba su karɓi katinan su ba, su garzaya ofisoshin hukumar zaɓe da ke ƙananan hukumomi da kuma hedkwatar hukumar don amsar katin zaɓe.

Ku tuntuɓi hukumar zaɓe ta INEC don samun cikakken bayani kan sabbin rumfunan zaɓe da aka ƙirkiro kusa da ku da ku. Haƙƙin kowanne mai kaɗa ƙuri’a ne sanin waɗannan sabbin rumfunan zaɓe, da aka ƙirkiro kusa da ku a mazaɓunku. Haƙƙin kowanne mai kaɗa ƙuri’a ne sanin waɗannan sabbin rumfunan zaɓe, don gudanar da zaɓe cikin sauƙi mafi kusa da ku a mazaɓun ku, cikin sauƙi da aminci.

Ƙungiyar JNI haƙiƙa tana kiran da a fita yin rijistar zaɓe gadan gadan. A karɓi katin zaɓe da ke jiran masu shi a ofisoshin hukumar zaɓe, kana a nemi sanin sabbin rumfunan zaɓe da aka ƙara kusanto da su ga jama’a.

Wannan saƙo ne daga Babban Sakataren Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta ƙasa, Dr Khalid Abubakar Aliyu.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts