Na naɗi bidiyon tsiraici na ne domin na rinƙa kalloa waya ina jin daɗi- Safara’u


Korarriyar jarumar cikin shirin Kwana Casa’in Safara’u Nura wadda asalin sunanta Safiyya Yusuf, daga ƙarshe ta yi bayani kan bayyanar bidiyon tsiraicin ta.

Jarumar, wacce ta koma yin waƙa, naɗaɗden bidiyon tsiraicin na ta ya bayyana ne a shekarar 2021, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar cireta daga shirin Kwana Casa’in mai dogon zango na tashar Arewa24.

A hirar ta da BBC Hausa cikin shirin Daga Bakin Mai Ita da ake hira da jarumai, Safara’u ta bayyana cewa bayyanar bidiyon ba yadda cewa yadda mutane suke tunani akan bidiyon, cewa ita ƴar maɗigo ce ko kuma wani saurayin ta ta aika wa bidiyon, ba haka bane.

Ta bayyana cewa, ta kan naɗi irin wannan bidiyoyin da dama ta ajiye a wayarta domin ta riƙa kallo lokaci zuwa lokaci ta na jin daɗi. A cewar ta, “kaso saba’in cikin ɗari na mata na irin wannan bidiyon su ajiye a wayar su”.

Sai dai, ta ce bayyanar bidiyon ya tada mata hankali matuƙa, lamarin da ya jefa ta cikin wani mawuyacin hali na kusan watanni uku amma daga ƙarshe mahaifiyarta da mahaifinta sun rarrsesheta da cewa ta ɗauki abin da ya faru a matsayin ƙaddara.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts