Muna amfani da labaran karya wurin bata sunan kasarmu a idon duniya- Pantami – Hausa Daily Times


Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna fargabar cewa kasar nan na rasa kimarta a kullum ta dalilin yada labaran karya.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a wajen wani taron ministoci na makon yada labarai da wayar da kan jama’a na UNESCO da ke gudana.

Da yake magana a taron, Mista Pantami ya bayyana damuwarsa game da yadda kafafen yada labarai suka fitar da wasu munanan bayanai marasa tushe game da Najeriya.

Ya ce lamarin yana shafar tunanin da duniya ke yi wa kasar mara kyau da kuma dakile zuba jari da ci gaba.

Mista Pantami ya ce bullowar sabbin kafafen yada labarai ya kara dagula al’amuran rashin gaskiya da labaran karya da kuma fahimtar kafafen yada labarai a duniya.

A cewarsa, da sabbin kafafen yada labarai, kowa ya zama dan jarida yayin da jama’a za su zauna a gidajensu suna hada duk abin da suka ga dama, ba tare da tankade da reraya ba kafin yadawa.

Ministan ya ce abin takaici ne yadda mutane ke rayuwa a cikin duniyar da labarai marasa dadi suke yaduwa kamar wutar daji.

Ministan ya ba da misali da wani lamari na baya-bayan nan inda ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwar tsaro kan hadarin hare-haren ta’addanci a Najeriya.

Ya ce ba tare da tantancewa ko la’akari da illar irin wannan sako ba, kafafen yada labarai ba suna yada bayanan kyauta.

Mista Pantami ya yi gargadin cewa kasashen da suka ci gaba da ke bayar da sanarwar tsaro da ba a tantance ba suna da nasu kalubale na tsaro, ciki har da harbe-harbe a makarantu amma suna gudanar da shi yadda ya kamata.

Wajen magance kalubalen, ministan ya ba da shawarar sake fasalin al’umma wanda zai fi mai da hankali kan sarrafa kai.

Ya ce dole ne ‘yan jarida su farka kan nauyin da ya rataya a wuyansu, su fahimci cewa aikinsu ya danganci aiki da gaskiya da rikon amana.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts