Mun shirya ci gaba da yajin aiki har sai mun samu abin da muke buƙata – ASUU


Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta ce mambobinta za su ci gaba da jajircewa wajen samun abin da jami’o’in gwamnati ke buƙata daga Gwamnatin Tarayya don gogayya da jami’o’in duniya.

Farfesa Ayo Akinwole, shugaban kungiyar ASUU na jami’ar Ibadan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ibadan.

Mista Akinwole ya ce malaman jami’o’in gwamnati a Najeriya na amfani da jininsu wajen tafiyar da jami’o’in gwamnati da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu.

“Malamai sun rike jami’o’in gwamnatin Najeriya da jininsu, amma ya dace ‘yan Najeriya su ce su mutu a bakin aiki? Muna bin su bashin alawus na sama da shekaru takwas ba su biyamu ba.

“Shin ASUU ne kawai ke yajin aiki? Wasu sassa (cibiyoyin bincike) na ƙasar nan sun shafe watanni 13 suna yajin aiki kuma gwamnati na biyansu albashi”.

A cewarsa, kungiyar ba za ta sadaukar da rayuwar mambobinta ba. Kuma za ta bijirewa duk wani yunƙuri na mayar da su zuwa bayi.

Ya ce ƙungiyar ta bayar da sanarwar yajin aikin na watanni 14 ga Gwamnatin Tarayya kafin fara yajin aikin a shekarar 2022.

Mista Akinwole ya ce, hatta kokarin da ƙungiyar addinai ta Najeriya ta yi a shekarar 2021 bai haifar da wani sakamako ba kafin a tilasta wa kungiyar ta ayyana yajin aikin a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Mista Akinwole ya ce Naira tiriliyan N1.1trn da ƙungiyar ke nema na farfaɗo da jami’o’i ba na malamai ba ne.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kai wannan adadin ne ta hanyar rahoton tantancewa a kan yawan lalacewar Jami’o’in Gwamnatin Najeriya.

Mista Akinwole, ya godewa mambobin ASUU bisa sadaukarwa da kuma ci gaba da jajircewa wajen mayar da ilimin jami’o’in ƙasar nan.

Ya ce yajin aikin ne kawai ya tilastawa gwamnati kashe kudaɗe a jami’o’in ta a cikin shekaru 25 da suka wuce.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts