Ministan Kwadago ya kira ma kansa ruwa, APC na neman ya yi murabus – Hausa Daily Times


Mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa Murtala Ajaka ya bukaci ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ya yi murabus idan har ba zai iya fitowa fili ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ba.

Ministan kwadagon, a yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, a ranar Juma’a, ya ki amincewa da Mista Tinubu, yana mai cewa zai zabi duk wanda ransa ke so a ranar zabe.

Da mai gabatar da shirin ya matsa masa lamba ya bayyana dan takarar da yake so tsakanin dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, da dan takarar jam’iyyar APC, ministan ya ce tambaya ce mai wahala, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin abokansa.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Mista Ajaka ya ce abin takaici ne ga Mista Ngige, wanda ke rike da mukamin minista a gwamnatin APC, ya yi irin wannan maganar.

Ya kara da cewa duk wadanda aka nada dole ne su ajiye burinsu a gefe su yi kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara ko kuma su yi murabus.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An dade da kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa kuma jam’iyyar ta yanke shawarar zabar Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, don haka ya kamata dukkan jagororin jam’iyyar su ajiye burinsu a gefe su dukufa wurin ganin nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar,” mataimakin. A cewar mataimakin Kakakin

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts