An yi gaggawar kai wani dan majalisar India (Minista) wani babban asibiti a New Delhi bayan ya sha ruwan kududdufin da ke mazabarsa don tabbatar wa mutanen yankin cewa ruwan bai da wata matsala idan suka sha.

Jaridar New Indian Express ta ruwaito dan majalisar mai suna Bhagwant Mann, Babban Ministan Punjab, an garzaya da shi zuwa asibiti a New Delhin ne bayan shan kofi daya na ruwan kogin Kali Bein da a cewar sa bata da wani illa.
- Buhari bai san ma an yi barazanar kama shi ba sai da na fada masa- Gwamna El-Rufa’i
- Naira ta yi mugun faduwa a kasuwar bayan fage, ta kai $1/N710
Bayan kwana biyu da shan ruwan, Mann ya fara korafin ciwon ciki.
An kai shi Asibitin Apollo Indraprastha da ke Sarita Vihar inda aka kwantar da shi cikin dare, sai dai sakamakon gwaje gwajen likitoci ya nuna Ministan ya kamu da cuta kuma kwararrun likitoci sun duba shi kafin aka sallame shi.
Sai dai dawowarsa gida ke da wuya cikin nashi ya ki, wanda ya tilasta gaggawar wucewa da shi zuwa wani asibiti a New Delhi, Babban birnin kasar domin samun cikakken kulawa.
Related