Ku yi hakuri da batun zanga-zangar da za ku yi- Gwamnatin Tarayya ga NLC


Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC da ta soke zanga-zangar da ta shirya yi kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i da sauran kungiyoyin jami’o’i suke yi.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya yi wannan roko a ranar Alhamis a wani taro da shugabannin kungiyar NLC a ofishin sa.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo da babban sakataren ma’aikatar Kachollom Daju.

A nasa jawabin, Ngige ya yi karin haske ga shugabannin kwadagon kan kokarin da gwamnatin tarayya ta yi kawo yanzu na warware matsalar da ke faruwa a jami’o’in, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da kokarin.

A ranar 17 ga watan Yuli ne kungiyar NLC ta sanar da cewa za ta fara zanga-zanga a fadin kasar a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin matsawa gwamnatin tarayya lamba kan ta warware yajin aikin da ASUU da sauran kungiyoyin jami’o’i suka yi na tsawon watanni biyar.

A wata takardar sanarwa dauke da sa hannun shugaban sashen hulda da jama’a na Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi ta Tarayya, Olajide Oshundun ya fitar, ministan ya tunatar da shugabannin kungiyar ta NLC cewa ya shigar da su cikin sulhun bangarorin uku da ke gudana a ma’aikatar sa, domin idan kungiyar ta san irin kokarin da gwamnati ta ke yi don warware matsalar, ba za su yi zanga-zangar ba.

Ya kuma shaida wa shugabannin kwadagon cewa Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta umarce shi da ya sanar da su mummunan illolin tsaro da zanga-zangar da aka shirya yi ke tattare da su.

A cewarsa, rahoton tsaro da hukumar DSS aikewa ofishinsa, ta yi kakkausar gargadi kan gudanar da zanga-zangar wadda aka shirya yi a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts