KNUPDA ta rushe ginin Masallaci da Islamiyya a Zawaciki


Nasiru Yusuf
Hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta rushe wani Masallaci da makarantar Islamiyya wanda mazauna Sabuwar Zawaciki dake yankin Karamar Hukumar Kumbotso suke ginawa.

Wadanda aka yi rusau din a gabansu sun shaidawa jaridar ALL IN ONE cewa da sanyin safiyar ranar Alhamis ne Ma’aikatan KNUPDA bisa rakiyar ‘Yan sanda da ‘Yan KAROTA dauke da bindigogi da sanduna suka yi wa unguwar dirar mikiya suka fara rushe ginin Masallaci da Islamiyya da al’umma suka yi karo-karo suke ginawa.

Shugaban Kungiyar mazauna unguwar Sabuwar Zawaciki Umar Faruk Inuwa ya ce a ranar Alhamis da misalin karfe 7:30 na safe an kira shi a waya aka shaida masa Ma’aikatan KNUPDA sun zo da Katafilar ‘yan sanda da ‘yan KAROTA suna rushe ginin Masallaci da Makaranta a filin da gwamnati ta ware don wannan gini.

“Yan sanda da uniform a jikinsu da MOPOL da uniform din su a jikinsu da ‘yan KAROTA ga civil defense kuma suna dauke da bindiga. Suka hana kowa bin hanyar masallacin.

“Mun yi kokari mu je land mu kar6i takardun filin saboda irin wannan, amma sai aka ce mana ba a bawa community takardun irin wannan filayen.

Wani makocin Masallacin mai suna Malam Ahmad ya ce da ma an ware filin ne don gina makaranta, hakan ya sa mazauna unguwar suka yi karo-karo suka fara ginin.

Malam Ahmad ya ce “Gwannati ce ta ware wurin don al’umma su mora. Mai taro mai sisi muka hadu muke wannan gini, domin ‘ya’yanmu da jikokinmu da sauran al’umma su mora.”

Jami’in Hulda da jama’a na Kungiyar mazauna Sabuwar Zawaciki Abba Darawa ya ce

“A ranar Alhamis mun tashi da wani ibtila’i da ya same mu a wannan unguwa ta mu ta Sabuwar Zawaciki. Mun fara kai yara Makaranta, sai ga Katafilar KNUPDA da rakiyar motocin ‘yan sanda da KAROTA suka rushe mana Masallaci Makarantar da muke ginawa.

“Gwamnatin nan ta tara al’ummar unguwa ta nuna musu ga filin makarantu ga na masallaci.

“Bukatarmu shi ne zalincin da aka yi mana da cin zarafin da aka yi mana da hadin kan wasu 6ata gari shi muke bukata a bit mana hakkinmu. An kashe miliyoyin kudi a wannan gini, amma yanzu an cuce mu an rushe. Sun bi mu da duka har da harbi sai ka ce tumakai.

Mazauna unguwar sun kewaya da wakilin ALL IN ONE inda yara ke karatu a gindin bishiya da rumfar kwano a kusa da inda aka rushe ginin makarantar.

Sun ce ajujuwan da KNUPDA ta rushe su ne ake sa ran yaran za su rika yin karatu a cikinsu.

Sai dai kuma mataimakin Darekata mai kula da sashen gine-gine a Hukumar KNUPDA Aliyu Dada, ya shaidawa ALL IN ONE cewa  sun rushe ginin ne don an yi shi ba akan ka’ida ba.
Dada ya ce, duk da cewa an ware filin ne don gina makaranta, amma tuni gwamnati ta ba wa wani mutum filin ya gina makaranta.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts