Kasuwar Jos: Majalisar Dokokin jihar Filato ta buƙaci gwamnati ta yi wa matasa bayani


Daga Abba Abubakar Yakubu

Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta buƙaci jama’ar jihar su kwantar da hankalin su game da yarjejeniyar haɗin gwiwar da gwamnatin jihar ta shiga da bankin JAIZ, domin sake gina babbar kasuwar Jos da ta ƙone.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar kan Watsa Labarai, Na’anlong Daniel, shi ya yi kiran haka a yayin da yake tsokaci amsa tambayoyin manema labarai a Jos, game da wannan yarjejeniya ta shekaru 40 da bankin JAIZ zai riƙe Babbar Kasuwar.

Na’anlong wanda shi ne yake wakiltar mazaɓar Mikang a majalisar ya bayyana cewa matasan jihar na da hakkin nuna rashin amincewar su da wannan yarjejeniya da ba su fahimci amfanin da za ta yi musu ba.

Ya ƙara tabbatar da cewa, idan gwamnati ta yi wa matasan da ke nuna rashin jin daɗin su gamsasshen bayani yadda ya dace, za su fahimci ribar da jihar za ta samu daga wannan haɗin gwiwa na sake gina wannan Babbar Kasuwa ta zamani.

Da yake kira ga Majalisar Zartarwa ta jihar da ta samar da muhallin tattaunawa da jama’ar jihar, don faɗakar da su amfanin da wannan aikin zai kawo jihar, ɗan majalisar ya gargaɗi jama’a su guji siyasantar da duk wani tsari na gwamnati, domin yin hakan zai riƙa mayar da jihar baya.

Mai magana da yawun bakin majalisar ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatin jihar za ta sa ido wajen yadda za a raba shagunan da za a samar, don a tabbatar an yi adalci kuma ba a ware kowanne ɓangaren al’umma ba, kuma duk wanda ya cancanta ya samu za a bashi ba tare da la’akari da ƙabilar da ya fito ko addinin sa ba.

Dangane da batun riƙon kasuwar da bankin zai yi na tsawon shekaru 40 don cire kuɗaɗen da ya kashe wajen sake ginin kasuwar, shugaban masu rinjayen ya ce gwamnati ba sayar da makomar jihar ta yi ba, kasuwar na nan a matsayin mallakin gwamnati kuma ita ce za ta jagoranci tafiyar da kasuwar.

Ya yi kira matasan Filato su ɗauki wannan yarjejeniya a matsayin wata dama da za su bunƙasa kasuwancin da basirar su yadda za su ci moriyar sake gina kasuwar da ke da amfani mai yawa.

Idan za a iya tunawa Gwamnatin Jihar Filato ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da bankin JAIZ don sake gina Babbar Kasuwar, wanda ya jawo muhawara mai zafi a cikin jihar.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts