Jami’ar jihar Neja ta yi watsi da yajin aikin ASUU, ta sanar da ranar komawar ɗalibai


Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) ta umarci ɗalibanta su dawo makaranta domin fara karatun zango na biyu daga ranar 5 ga watan Satumban 2022.

Cikin wata sanarwa da mataimakin Rajistrar jami’ar Alhaji Baba Akote ya fitar, ya ce hukumar gudanarwar jami’ar ta amince da bude makarantar ne a zamanta na 55 a yau Talata.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ana tsammanin dukkan Malaman jami’ar su koma bakin aiki rana ɗaya da ɗalibai.

Jami’ar IBBUL dai ta bi sahun Jami’o’in jihohi da suka yi wa ASUU tutsu na kin ci gaba da yajin aiki biyo bayan kalaman shugaban kungiyar na ƙiran jami’o’in “marasa amfani”.

Tuni dai ɗaya daga cikin Malaman Jami’ar Farfesa Muhammad Aliyu Paiko ya sanar da ficewa daga ƙungiyar.
Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts