Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato ta ƙulla ƙawancen inganta rayuwa


Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sakkwato

Hukumar kula da tattara Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato za ta cigaba da haɗa gwiwa da hukumomi, ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a domin samar da tallafin kuɗi yin wasu ayyuka na moriyar jama’a.

Shugaban hukumar, Malam Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato shi ya bayyana haka a yayin da yake ƙaddamar da wani shirin inganta lafiyar al’umma mai rassa uku, da aka yi wa laƙabi da Lahiya Sak, ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa da ofishin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Bodinga, Dange-Shuni da Tureta, Dr. Balarabe Shehu Kakale.

A yayin ƙaddamar da shirin haɗin gwiwar wanda aka gudanar harabar fadar Hakimin Ɓodinga, shugaban Hukumar SOZECOM, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya sanar da cewa, ɗan majalisar ya ba da motocin ɗaukar marasa lafiya guda uku da za a ajiye ɗaya a kowacce ƙaramar hukuma da ke yankin mazaɓarsa, don inganta lafiyar al’ummar sa.

Ya ce, an ba wannan tallafi ne ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko wata wariya ba.

Wakilin Dr. Balarabe Shehu Kakale ya bayyana cewa, wannan tsari wani ɓangare ne na shirin Kiwon Lafiya na Waƙafi, da zai tallafawa mutane dubu huɗu masu buƙatar tallafin lafiya a cikin mazaɓarsa.

Ya buƙaci Hakiman da suka fito daga ƙananan hukumomi uku da shirin tallafin ya shafa, su kafa kwamitocin kula da Aikin Kiwon Lafiya na Waƙafi a yankunan su, domin tabbatar da yadda aikin ke tafiya.

A jawabin sa, Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Muhammad Ali lnname ya yabawa wannan ɗan majalisa, tare da kira ga sauran ýan siyasa da su riƙa tallafawa ƙoƙarin da gwamnati take yi a harkar lafiya, da kuma tabbatar masa da samun cikakken haɗin kai da goyon bayan gwamnatin jihar.

A saƙon sa na sanya albarka ga wannan aiki, Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci Dr. Umar Altine Dandin-Mahe ya bayyana cewa tsarin Waƙafi, yana samar da cigaban tattalin arziƙi a akasarin ƙasashen Musulmi da ke amfani da wannan tsarin, don haka ya ba da shawarar a yi amfani da shi wajen kula da inganta rayuwar Almajirai da Marayu.

A cikin jawabin su na godiya, Shugaban Ƙaramar Hukumar Boɗinga Alhaji Shehu Muhammad Ɗan Malikin Ɗanchadi, da Hakimin Boɗinga Alhaji Bello Abdurra’uf, sun yi godiya ga Hukumar Zakka da Waƙafi ta jiha, da ɗan majalisar su Dr Balarabe Kakale, bisa wannan tallafi da suka samu.

Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato SOZECOM ta ɓullo da wannan tsari ne mai rassa uku ne da ya shafi ɓangaren Kula da Kiwon Lafiya ƙarƙashin tsarin inshorar Musulunci na Waƙafi, sai tsarin samar da motocin ɗaukar marasa lafiya, da kuma tsarin inganta harkokin sufuri da kare aukuwar haɗurra.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts