Har yanzu Allah bai nuna min wanda zai zama Shugaban Najeriya na gaba ba – Fasto Kumuyi – Hausa Daily Times


Babban Malamin Cocin nan na Deeper Life, Fasto William Kumuyi, ya ce bai taba samun wani wahayi daga Allah dangane a da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba ba.

Sai dai ya yi alkawarin bayyanawa da zarar Allah ya nuna mishi wanda zai zama shugaban Najeriya. Kumuyi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a Minna yayin babban taron cocin na duniya.

“Ba zan iya gaya muku ƙarya ba. Allah bai nuna min komai ba. Kila bai ga ya dace ya sanar da ni yanzu ba. Ba kowa ya ke gaya wa komai ba. Waye ni da zan gaya wa Allah, me ya sa bai nuna min wanda zai zama Shugaban kasa na gaba ba? Idan ya sanar da ni zan zo in sanar da ku.”

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts