Gwamnonin APC na barazanar yi wa takarar Tinubu zagon kasa a 2023 – Hausa Daily Times


Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun yi barazanar yin zagon kasa a yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyarsu da dan takararta, Bola Tinubu a jihohinsu.

Gwamnonin kqrkashin kungiyareubta PGF, sun zargi jam’iyyar da dan takararta, Bola Tinubu, da yin watsi da nade-naden da suka yi a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.

A ranar Asabar ne sakataren kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC, James Faleke, ya bayyana lsunayen yan Majalisar Yakin Neman Zaben , inda ya bayyana sunayen mutane 422 da suka hada da wadanda za su yi aiki a matakin shiyya da jiha domin nasarar Bola Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima a 2023.

Kafin nan dai shugabannin jam’iyyar sun tuntubi gwamnonin ta kungiyarsu ta PGF domin tantance wasu mutane a jihohinsu da za su zama mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa cewa gwamnonin da su mika sunayen mutane biyar, kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai, akwai jihohin da mutanen da sunayen su ya fita basu fika adadin mutanen da aka mika sunayen su ba.

Gwamanan jihar Cross River da Kwara Ben Ayade da Abdulrahman Abdulrazaq na daga cikin wadanda ke barazanar ficewa daga Majalisar Yakin Neman Zaben jam’iyyar. Ayade ya ce, babu sunan mutum daya dada cikin sunayen mutane biyar da ya gabatar da ya fito a sunayen da jam’iyyar ta fitar, yayin da Abdulrazaq ya ce sunan mutum daya kawai ya fito a jihar sa.

Shi ma Gwamna Rotimi Akeredelu na jihar Ondo, wanda ya bayyana a jerin sunayen a matsayin Kodinetan yakin neman zaben yankin Kudu maso Yamma, ya koka da shugabannin jam’iyyar cewa an yi watsi da sunayen mutanen da ya gabatar.

A yankin Arewa kuwa, wasu gwamnonin APC na cewa Bola Ahmed Tinubu ya kasa tafiyar da su a tafiyar yakin neman zabensa kawo yanzu. Tsoron gwamnonin shine “Dan takarar shugaban kasar ya gagara aminta da daya daga cikinsu banda na kusa da shi.”

Gwamnonin, musamman na yankin Arewa maso Yamma, na ganin makomar siyasarsu ba za ta yi kyau ba a hannun Tinubu, wanda suka zarga da mayar da su gefe. Suna ganin yadda ya gudanar da jerin sunayen majalisar yakin neman zaben ya nuna cewa bai mutunta kungiyar gwamnonin ba.

Masana siyasa sun fara bayyana cewa  wannan rashin jituwar na samar da damammaki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, na samun marawar baya daga gwamnonin jam’iyyar APC.

Gwamnonin musamman na Arewa-maso-Yamma, an ce suna barazanar janye goyon bayansu idan har aka ci gaba da yin watsi da su.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts