Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da wata sabuwar kungiyar ASUU – Hausa Daily Times


A wani yunƙuri na gwamnatin tarayya na datse fikafikan ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU, gwamnatin a yau Talata za ta gabatar da takardar shaidar rajista ga sabuwar ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya wato “Congress of Nigerian University Academics” (CONUA), da wasu ‘yan ƙungiyar ASUU da suka balle suka kafa.

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi Chris Ngige ne zai gabatar da takardar.

Hakan na kunshe ne a wata gayyata da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Kwadago Oshundun Olajide ya aikewa manema labarai a ranar Talata.

CONUA, wasu membobin Kungiyar ASUU ne suka kafa ta bayan sun balle, kuma tana da membobi a wasu jami’o’in gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Kodinetan ta na kasa, ‘Niyi Sunmonu, malami a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts