Gwamnatin tarayya na shirye-shiryen buɗe jami’o’i duk da yajin aikin ASUU


Alamu na nuna cewa, duk da ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, na ci gaba da yajin aikin da take yi, gwamnatin tarayya na shirin sake buɗe jami’o’in da ke a ƙulle.

Majiya mai tushe daga ma’aikatar ilimi ta tarayya ta bayyana wa jaridar Vanguard  cewa ba malaman jami’o’in ne kaɗai ke aiki a cikin jami’o’in ba, don haka tun da ma’aikatan jami’o’in da ba na ilimi a  shirye suke su koma bakin aiki, bai kamata a ci gaba da rufe jami’o’in ba.

“Bugu da ƙari, akwai wasu malamai waɗanda su ma a shirye suke su koma yi aiki, bai kamata irin wadannan ma’aikata a hana su ba. A kwanakin baya akwai wata kungiya ta yi wa manema labarai jawabi a Abuja, inda ta ce ba sa cikin matsalar ASUU. Kungiyar su ma tana aiki don a yi musu rajista a hanzu haka.

“Ma’aikatan da ba na koyarwa ba suma sun janye yajin aikin da suke yi kuma jami’a ba na ma’aikatan ilimi ne kawai ba. Me ya sa za a hana wadanda ke shirin yin aiki damar yin aiki?”. A cewar majiyar.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da taron shugabannin jami’o’in gwamnatin tarayya a ranar Talata mai zuwa a hukumar kula da jami’o’i ta kasa, NUC da ke Abuja.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts