Garin yakar rashawa, sai ita ta yake ni har ta fidda ni EFCC- Magu – Hausa Daily Times


Tsohon shugaban riko na hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana ficewar sa daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa da cewa rashawar ce ta yake shi.

Mista Magu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja a wajen bikin karramawar da kungiyar dalibai mata ta Arewa ta shirya domin karrama shi.

“Ni rashawa ce ta yakeni yayin yakarta; amma ina farin ciki cewa abubuwan da suke faru a baya-bayan nan suna bayyana gaskiya ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.

Mista Magu wanda ya samu wakilcin dansa, Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu ya godewa kungiyar bisa karrama shi da ta yi kuma ya ce ya yi farin ciki da hakan.

A’isha Nasir, mai magana da yawun kungiyar da ta kunshi dalibai mata na jami’o’i a sassan arewacin Najeriya, ta bayyana cewa an zabi Mista Magu ne domin karramawar saboda sadaukar da kai wajen hidamtawa kasa.

“Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya aiki ne mai daure kai wanda ke bukatar ganin bayan siyasa ko makamanciyar haka.

“Ku ƙaunace shi ko ku ƙi shi, Ibrahim Magu ya ɗauki yaƙi da cin hanci da rashawa zuwa matakin da ba a san shi ba inda mutane da yawa ke tunanin ba za a iya kaiwa ga nasara ba.

“Magu ya samu yabo na nahiyoyi da na duniya kan yadda ya magance abin da aka bayyana a matsayin babban abin da ke kawo cikas ga ci gaba kasashen Afirka da tattalin arziki,” in ji mai magana da yawun kungiyar.

Karramawar ta zo ne a kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta yanke a ranar 4 ga watan Oktoba wanda mai shari’a Yusuf Halilu ya yanke.

Mai shari’a Halilu ya wanke Magu daga zargin cewa Fasto Emmanuel Omale na Divine Hand of God Prophetic Ministry, da matarsa, Deborah sun boye Naira miliyan 573 na tsohon shugaban EFCC.

An zargi Faston da amfani da kudin ne wajen saya wa Mista Magu kadarori a Dubai.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts