Da ya hallaka iyayen shi saboda kudi a jihar Anambra – Hausa Daily Times


Wani matashi dan shekara 21 mai suna Chukwudi ya kashe mahaifiyarsa da mahaifinsa a garin Nnewi na jihar Anambra.

Wanda ake zargin da aka mishi shaidar shay-shaye, shi ne da daya tilo ga iyayen shi.

An tsinci gawarwakin iyayen a gidansu bayan sun fara yin wari, inda aka samu gawarwakin da alamun an sassarasu ne da adda, a ranar Alhamis, 22 ga Satumba, 2022.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya kashe iyayensa ne bayan da suka yi zazzafar cacan baki tsakanin su bisa rashin bashi kudi da ya bukata daga garesu.

Ana zargin dan mai suna Chukwudi ne da kashe iyayensa na shi kwanaki kafin ya gudu zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa makwabta ne suka gano gawarwakin, bayan sun fara jin bakon wari daga dakin kwanan su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a 23 ga watan Satumba, ya ce sun kaddamar da fara farautar wanda ake zargin.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts