Da Dumi-Dumi: Sojoji sun hallaka kasurgumin dan fashin daji da mayakansa a Kaduna – Hausa Daily Times


Sojojin Najeriya sun hallaka wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga a jihar Kaduna, Ali Dogo da wasu manyan yaransa 30 a wani hari da suka kai ta sama a karshen makon jiya.

Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya mai tushe ta soji ta tabbatar mata cewa Dogo, wanda aka fi sani da Yellow, tare da ‘yan yaransa, an hallaka su ne sakamakon harin da rundunar sojin sama ta kai.

Yayin da ta ke tabbatar da yadda aka yi wa Yellow da mayakansa ruwan bama-bamai, majiyar ta bayyana cewa kasurgumin shugaban ‘yan fashin tare da mutanensa sun tsere ne daga jihar Neja zuwa gidan wani Alhaji Gwarzo da ke garin Yadi a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna domin tsira da rayukansu, biyo bayan harin da jirgin sojin sama ya kai masa a inda yake a Neja, kwanan nan.

Majiyar ta kuma kara da cewa, wasu jiragen sojin sama sun kai wasu hare-hare na daban kan ‘yan ta’adda a wani wuri mai nisan mita 33 daga Arewa maso yammacin Mando a Kaduna, inda nan ma aka musu ruwan bama-bamai.

Da yake tabbatar da nasarar da suka samu a hare-haren da aka kai, mai magana da yawun Rundinar Sojin Saman Najeriya, Kwamando Edward Gabkwet, ya ce rundunar za ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a yankin Arewa maso Yamma.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts