Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin buɗe jami’o’i domin fara karatu – Hausa Daily Times


Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar jami’o’i ta kasa ta umurci shugabannin jami’o’in da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu.

Hakan ya fito ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan kudi na NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar Farfesa Abubakar Rasheed.

Wasikar wacce ta bayyana a ranar Litinin, an aika ta ga dukkan Shugabannin jami’o’in na kasa.

“Tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU nan da nan suka koma/fara laccoci; Maido da ayyukan yau da kullun da na yau da kullun na cibiyoyin jami’o’i daban-daban”, a wani bangare na wasiƙar.

Jaridar Hausa Daily Times ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata ne kotun Da’ar Ma’aikata ta Najeriya ta umarci Kungiyar Malaman Jami’o’i da ta janye yajin aikin da take yi a fadin kasar.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki domin matsa lamba kan bukatar inganta kudaden da ake baiwa jami’o’in, da batun albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.

An dai kawo karshen tarukan da aka yi tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya cikin rashin jituwa.

Sakamakon haka gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.

Gwamnati ta bakin lauyanta, James Igwe, ya roki kotun da ta dakatar da ASUU daga daukar wasu matakai dangane da yajin aikin, har sai an yanke hukunci kan karar.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts