Da Dumi-Dumi: BBC za ta yi sabbin sauye-sauye – Hausa Daily Times


Hukumar Kula da Kafafen Yada labarai ta kasar Birtaniya (BBC) ta fara shirin rufe wasu watsa shirye-shiryen Sashen Hausa a wani kokarin sauya tsarin watsa shirye-shiryen ta gaba daya daga talabijin da rediyo zuwa tashoshi na zamani.

Ba wai iya BBC Hausa kadai matakin zai shafa ba, har ma da sauran gidajen rediyo da talabijin, da suka hadar da gidan talabijin na Somali TV da tashoshin talabijin na Afrique, wadanda suka zama amintattun hanyoyin samun ingantattun bayanai ga al’ummar Afirka.

Shirye-shiryen al’amuran yau da kullun wato ‘Focus on Africa’, wanda aka saba gabatarwa sama da shekaru 50, za a canza shi zuwa tsarin ‘podcast’.

Sauran shirye-shirye cikin harsunan Afirka kuma za a mayar da su zuwa shirye-shiryen zamani, sannan za a dakatar da wasu shirye-shiryen yara.

A ranar 29 ga watan Satumban 2022 ne BBC ta sanar da fara daukan wasu sabbin sauye sauye, inda ta ce za ta daina shirye-shiryen rediyo cikin wasu harsuna a gadin duniya tare da maida wasu shirye-shiryenta a intanet zallah.

Wasu daga cikin harsunan da za a dai shirye-shiryen radio da su a akwai Kyrgyz, Uzbek, Hindi, Indonesian, Tamil, da Urdu.

Wadanda za su komar da su yanar gizo-guzo kawai sun hada da Chinese, Gujarati, Igbo, Indonesian, Pidgin, Urdu, and Yoruba.

Da take kare matakin, BBC ta bayyana cewa canjin ya zama dole don dacewa da bukatu da dabi’un masu sauraronta.

“Bukatun masu sauraro da halaye suna canzawa, kuma mun san cewa akwai yuwuwar ci gaban fasahar zamani a fadin nahiyar,” Mai magana da yawun BBC ya fada wa kafar Semafor.

Wakilin, duk da haka, ya ba da tabbacin cewa BBC har yanzu “ta himmatu wajen ci gaba da samarwa tare da watsa sahihan bayanai ga jama’a a fadin Afirka” kuma ba za ta daina yi wa masu sauraronta hidima a cikin harsunansu ba.

Wasu ma’aikatan BBC sun soki wannan mataki suna masu cewa ba dukkan ‘yan Afirka ne ke samun saukin shiga intanet ba, kuma kamfanin bai yi la’akari da irin makudan kudaden da mutane miliyan 63 ke kashewa ba wajen sauroron BBC a Africa.

Najeriya, Kenya, da Tanzaniya sun kasance uku daga cikin manyan masu sauraron kamfanin a Africa.

Sauye-sauyen na BBC zai haifar da babban hasara ga yawancin ‘yan jarida da ke aiki tare da kamfanin a Afirka.

Paul Siegart, wakilin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa a Burtaniya, ya roki ‘yan majalisar da su goyi bayan kira da suke yi ga mahukuntan BBC da su sake duba wannan mataki.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts