CBN zai sauya fasalin wasu takardun kudin Najeriya – Hausa Daily Times


Gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sanar da ce bankin zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin Najeriya guda uku.

Ya ce babban bankin ya samu amincewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin sauya fasalin takartun kuɗi na N200, da N500, da kuma N1000.

Ya ƙara da cewa sabbin kuɗin za su fara aiki ne ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe.

Mista mefiele ya ce ”daga yanzu an cire kuɗin da ake karba daga mutane a lokutan da suke zuwa saka kuɗi a banki.

Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar ana hada-hada da su ne ba ta hanyar bankin ba.

Ya ci gaba da cewa wannan mataki zai ƙara wa kuɗin kasar daraja.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts