An sake kama wani fursuna da ya tsere daga gidan yarin Jos

An sake kama wani fursuna da ya tsere daga gidan yarin Jos

Daga Habu Ɗan Sarki Kwamishinan ýan sanda na Jihar Filato, Bartholomew Onyeka ya sanar da sake kama wani riƙaƙƙen mai laifi da ya tsere daga Gidan Gyara Halinka na Jos cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, sakamakon wani hari da wasu ýan bindiga suka kai, wanda kuma ya […]

Tsohon shugaban ƙasa Babangida na goyon bayan gina Sabuwar Najeriya

Tsohon shugaban ƙasa Babangida na goyon bayan gina Sabuwar Najeriya

Daga Habu Ɗan Sarki Tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi alƙawarin cigaba da goyon bayan sa ga ƙungiyar Team New Nigeria, domin tabbatar da cikar burin manufofin kafa ƙungiyar. Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne yayin da yake tarbar tawagar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Dr. Modibbo Yakubun Farakwai wanda ya ziyarce shi a […]

Kasuwar Jos: Majalisar Dokokin jihar Filato ta buƙaci gwamnati ta yi wa matasa bayani

Kasuwar Jos: Majalisar Dokokin jihar Filato ta buƙaci gwamnati ta yi wa matasa bayani

Daga Abba Abubakar Yakubu Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta buƙaci jama’ar jihar su kwantar da hankalin su game da yarjejeniyar haɗin gwiwar da gwamnatin jihar ta shiga da bankin JAIZ, domin sake gina babbar kasuwar Jos da ta ƙone. Shugaban masu rinjaye na majalisar, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar kan Watsa Labarai, […]

ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni huɗu

ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni huɗu

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wasu ƙarin makwanni huɗu. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce sun ɗauki matakin ne domin baiwa gwamnati isasshen lokaci domin warware duk wata matsala da […]

Sakon gaggawa daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Sakon gaggawa daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta ƙasa wato JNI, ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na lll CFR, MNI, na kira da jan hankali ga waɗanda har yanzu ke jinkiri wajen yin rijistar katin zaɓe, da kuma matasa da suka kai munzalin mallakar katin zaɓe, da a hanzarta yin rijista kafin cikar wa’adin […]

Naira ta yi mugun faduwa a kasuwar bayan fage, ta kai $1/N710

Naira ta yi mugun faduwa a kasuwar bayan fage, ta kai $1/N710

Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar canjin kasashen waje na bayan fage, inda a yau Laraba dalar Amurka daya ($1) ya kai  N700, Hausa Daily Times ta gano. Hausa Daily Times ta gano cewa, yan canji a Abuja su na sayan dala $1 a kan N690, su nw sayarwa a kan N700. An […]

Sanatocin PDP na barazanar tsige Buhari in bai magance matsalar tsaro ba

Sanatocin PDP na barazanar tsige Buhari in bai magance matsalar tsaro ba

Mambobin jam’iyyar PDP a majalisar dattawan Najeriya sun ba wa shugaba Buhari wa’adin makonni shida da ya magance tabarbarewar tsaro a fadin kasar ko kuma a tsige shi. Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Phillip Aduda, ya bayyana matsayin ‘yan majalisar a ranar Laraba yayin da yake ganawa da […]

Wani jirgin ruwa ya sake hatsari da yan kasuwa a jihar Neja

Wani jirgin ruwa ya sake hatsari da yan kasuwa a jihar Neja

Mutum daya ya nutse, wani kuma ya samu rauni a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Nansa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja. Alhaji Ahmed Inga, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA) ne ya bayyana hakan a zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar […]