Buhari bai san ma an yi barazanar kama shi ba sai da na fada masa- Gwamna El-Rufa’i


Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce shi ne ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari game da barazanar da masu ikirarin jihadi suka yi cewa za su kama shugaban da shi gwamnan.

Gwamman ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida da ake yadawa kai tsaye, jiya Laraba da daddare, BBC Hausa ta ruwaito.

Idan dai ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne masu ikirarin suka fitar da wani biidiyo da ke nuna mutanen da suka sace na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, tun a watan Maris inda a ciki suke barazanar cewa sai sun kamo shugaban kasar da gwamnan.

El-Rufai ya ce shi Buhari bai ma san da wannan barazana ba sai da ya gaya masa, sannan kuma Gwamman Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ka wa shugaban hoton bidiyon ya gani.

Gwaman na jihar kaduna ya ce daman shi tun a baya an gargade shi da ya yi hankali shi da iyalinsa a kan wannan barazana.

Ya ce, ‘’Ta yaya za mu kasance a kasar da take da sojoji da ‘yan-sanda da gwamnatin tarayya amma kuma wasu ‘yan ta’adda su rika barazanar za su sace shugaban kasa?’’

Gwamnan ya ce ai shi daman tun baya da shekara biyar yake bayar da shawara da a shiga dajin a yi wa sansanoninsu ruwan bama-bamai, da cewa ta hakan ne za a yi maganinsu.

Ya ce ya gana da Shugaba Buhari ranar Lahadi inda ya gaya masa yadda girman wannan matsala ta tsaro yake.

Ya yi bayani da cewa, idan a baya wadanda ke cikin gwamnati suna daukar wannan abu da wasa, suna ganin abin na faruwa ne kawai a Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja, to yanzu abin ya zo har gida, saboda haka dole ne a tashi a ga bayan mutanen nan.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts