Buba Gabon, ɗan garuwa da aka kwace kurar sa don shi ɗan PDP ne


Wannan shi ne Buba Gabon, da Hausa Daily Times ta gano ya shafe sama da shekara goma ya na tura kurar ruwa (sayar da ruwa a amalanke) a garin Madagali na jihar Adamawa amma bai da na shi na kan shi.

Buba Gabon tsaye a gefen sabon Amalanken da aka bashi kyauta.

Wani mazaunin jihar Adamawa Alhaji Yaro Gulak ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa a kwanan nan mai amalanken da Buba Gabon ke turawa ya karbe abin shi bayan ya gano shi dan jam’iyyar PDP ne.

Wanda ya wallafa labarin ya ruwaito cewa wani dan siyasa a garin, Dan Maliki Madagali Alhaji Dauda Saidu a yanzu haka ya hada wa Gabon, sabon amalanke da jarakuna da kudin da aka kashe ya kai N82,000 ya mallaka masa kyauta.
Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts