Babu kobo da aka biya domin ceto fasinjoji 23 – Minista

Gwamnatin tarayya ta ce ba a biya ko sisin kwabo ba domin a sako sauran fasinjojin jirgin kasa 23 da aka yi garkuwa da su.

Gwamnatin tarayya ta kuma ce ana ci gaba da shirin dawo da aikin jirgin da aka dakatar nan ba da dadewa ba.

Sai dai ta ce za ta fito da waeu tsare-tsare nan da ‘yan watanni don tabbatar da tsaron layin dogo da fasinjoji.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka a Abuja, a wani taron manema labarai da aka shirya domin karbar fasinjoji 23 da aka sako.

Ma’aikatar ta yi nuni da cewa wadanda aka sako za su kasance a ma’aikatar amma bayan an shafe sa’o’i ana jira, ministan ya bayyana dalilin rashin zuwan nasu.

Da yake magana kan zargin biyan kudin fansa, ya ce: “Bai dace a bayyana ainihin matakan da aka dauka ba don ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

A cewarsa, ba a iya gane kansu ba tun da suka koma ga iyalansu a ranar Alhamis,

Abin da nake so in bayyana a nan shi ne, duba da cewa wannan gwamnati ba ta goyon bayan biyan kudin fansa, kuma ba ta amince da biyan kudin fansa ba, babu wani kobo da aka biya domin a sako wadannan mutane 23 da aka yi garkuwa da su da sauran su ma.”

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts