ASUU ta daukaka kara kan hukuncin Kotun Da’ar Ma’aikata – Hausa Daily Times


Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya, ASUU, ta daukaka kara a kan umarnin kotun Da’ar Ma’akata ta kasa da ta umurci malaman da ke yajin aiki su koma bakin aiki.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne Kotun Da’ar Ma’aikata ta umarci kungiyar da ta janye yajin aikin da ta ke yi na wata bakwai har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar.

Lauyan gwamnatin tarayya James Igwe, ya bukaci kotu ta tilasta wa malaman jami’o’in su koma bakin aiki har sai an warware musu bukatunsu na inganta aiyyukan su.

Kotun ta yi amfani da sashe na 18 na dokar rigingimun ma’aikata ta (TDA) ta samar da kuma bukatun dalibai ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na neman umarnin tilastawa ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe watanni bakwai tanw yi.

Da ta ke yanke hukunci kan bukatar, alkaliyar kotun, Mai Shari’a Polycarp Hamman, ta hana ASUU ci gaba da yajin aikin da take yi har sai an yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan ASUUn.

A nata jawabin, gwamnatin tarayya ta ce a karkashin sashe na 18 (1) E na TDA, ma’aikata ba za su iya ci gaba da yajin aiki ba yayin da aka mika wani batu zuwa Kotun Da’ar Ma’aikata don yanke hukunci, kuma akwai bukatar yin duba ga wannan lamari domin baiwa dalibai daman komawa karatu.

A cewar Lauyan, rashin janye yajin aikin zai haifar da barna maras misaltuwa ga daliban jami’a da ma kasa baki daya.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts