Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wasu ƙarin makwanni huɗu.
Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce sun ɗauki matakin ne domin baiwa gwamnati isasshen lokaci domin warware duk wata matsala da ta kunno kai da malaman.
- ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni huɗu
- Buba Gabon, ɗan garuwa da aka kwace kurar sa don shi ɗan PDP ne
Da yake lura da cewa ƙungiyar ta yi wani zaman gaggawa a jami’ar Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, shugaban kungiyar ASUU ya ce ƙarin wa’adin ya fara aiki nan take daga ranar 1 ga watan Agusta.
Related