An sako sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 23 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda – Hausa Daily Times


An sako sauran fasinjoji 23 da suka rage a hannun ‘yan ta’addan da suka sace su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

A wata takardar sanarwa da shugaban kwamitin shugaban kasa kan kubutar da fasinjojin Farfesa Usman Yusuf ya fitar, ya ce an sako wadanda harin ya rutsa da su ne da karfe 4 na yammacin Laraba.

“Na yi farin cikin sanar da al’umma da duniya cewa da misalin karfe (4:00pm) a yau Laraba 5-10-2022, kwamitin mutum bakwai na shugaban kasa wanda babban hafsan hafsoshin soji (CDS), Janar LEO Irabor ya kafa, ya tabbatar da sakin tare da karban sauran fasinjoji 23 da suka rage a hannun masu garkuwa da su. ‘Yan ta’addar Boko Haram da suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28-3-2022.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts