An naɗa ɗan’uwan Aisha Buhari shugaban Kamfanin buga kuɗin Najeriya


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Ahmed Halilu a matsayin Manajan Darakta Kamfanin buga kuɗi na Najeriya (NSPMC Plc).

Halilu, wanda yaya ne ga uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari, ya jagoranci kamfanin na riƙon ƙwarya na wasu watanni, tun bayan yin murabus na tsohon shugaban kamfanin Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban ya amince da nadɗin ne bayan shawarar Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

Mista Halilu ya na da gogewa a harkar banki, ya shafe sama da shekaru 23 yana aiki a wannan fanni inda ya yi aiki da African International Bank, AIB da Zenith Bank.
Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts