An kashe ‘yan Boko Haram a wani yunkurin kai hari domin kubutar da ‘yan uwansu a jihar Neja – Hausa Daily Times


Akalla ‘yan ta’adda takwas aka hallaka da ake zargin ‘yan Boko Haram ne tsagin ISWAP a yankin New Bussa na karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Wannan lamari ya faru ne a karshen mako mn jiya yayin da ‘yan ta’addan suka kai farmaki barikin soja a yankin don kubutar da ‘yan uwansu dake tsare.

A cewar wasu rahotanni, an kuma kama wasu tsageru uku daga cikinsu, sai dai an ruwaito cewa, wasu daga jami’an sojojin sun samu raunuka a rikicinsu da ‘yan ta’addan.

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Tribune Online cewa, ‘yan ta’adda sun farmaki barikin sojan ne a daren Asabar da misalin karfe 12 na dare yayin da suka yi kokarin kutsawa don ceto ‘yan uwansu dake tsare a ciki.

An tattaro cewa, sojojin da suka ji daga ‘yan ta’addan sun nemi taimakon sojin sama, wadanda daga baya suka zo suka ci karfin ‘yan ta’addan tare da fatattakarsu.

Wasu rahotanni sun ce, wasu ‘yan ta’adda da dama sun tsere da raunukan harbin bindigan da suka samu a fafatawarsu da sojojin.

A zantawan Hausa Daily Times da Sarkin Wawa Dr. Ahmad Aliyu, ya ce jami’an tsaro na ci gaba da yin nasarar kama sauran ‘yan ta’addan wadanda suka tsere a harin.

“Tun jiya Lahadi jami’an tsaro ke kama wasu daga cikin ‘yan ta’addan kuma ko yau kadai sun kama kusan 11”. A cewar Sarkin.

Garin na Wawa dai, nan ne barikin sojojin da ake tsare da ‘yan boko haram sama da 1669 da aka kama yake, wadanda suke zaman jiran shari’a.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts