An fara gano bakin zaren magance rikicin ASUU – Hausa Daily Times


Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta yabawa Majalisar Wakilai kan tsoma bakin da ta yi a rikicin ta da Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce, “A karon farko, sai yanzu muka fara ganin haske.”

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, wanda ya yi wa shugabannin kungiyar ASUU bayanin ganawar da suka yi da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan rikicin, ya ce yana sa ran za a janye yajin aikin cikin ‘yan kwanaki.”

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa kungiyar a shirye ta ke ta janye yajin aikin na watanni takwas.

Lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana, a ranar Litinin ya bayyana cewa ASUU a shirye take ta janye yajin aikin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Falana ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta kammala tattaunawa da kungiyar ta ASUU.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa ganawar da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da fadar shugaban kasa kan lamarin zai haifar da sakamako mai kyau.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts