Aisha Buhari ta nemi ‘yan Najeriya su yafe wa gwamnatin su kan tsadar rayuwa – Hausa Daily Times


Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro da aka fuskanta a gwamnatin Buhari.

“Mai yiyuwa gwamnatin ba a ji dadinta ba, amma ina so in yi amfani da wannan dama domin neman gafarar Malamai da ‘yan Najeriya baki daya. Muna bukatar dukkanmu mu hada kai domin samun ingantacciyar Najeriya,” Hajiya Aisha ta bayyana hakan ne a yayin taron addu’o’i da kuma lacca na musamman na ranar samun ‘yancin kai karo na 62 da aka shirya a dakin taro na masallacin kasa dake Abuja.

Aisha Buhari yayin bikin cikan Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Aisha, wanda ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’ar yin zaben 2022 cikin lumana, ta kuma ce tilas ne ‘yan kasar su hada kai don dawo da zaman lafiya a sassan kasar da suka fi fama da rikici.

Yayin da take yaba kokarin hukumomin tsaro na yaki da ta’addanci, ta ce ‘yan Najeriya dole ne su ma su hada kai su yaki kalubalen tsaro.

“Na yi farin ciki musamman yadda jami’an tsaron mu suka tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen tsaro fiye da kowane lokaci. Kuma a halin yanzu kokarin da suke yi na ci gaba da korar illar ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane da sauran miyagu a cikin al’umma.

“Na yaba da kokarin jami’an tsaron mu maza da mata kuma ina so in yi addu’ar don samun nasara a ayyukansu,” Aisha Buhari ta kara da cewa.

Domin karawa kokarin gwamnati na kyautata jin dadin ‘yan kasa, ta ce ofishinta ya samar da tsare-tsare da dama a fannonin noma, kasuwanci da hada kai da matasa da mata domin dakile illolin da samar da sauki.

Share:

Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on pinterest
Pinterest
Share on linkedin
LinkedIn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Get The Latest Updates

Subscribe To Our Weekly Newsletter

No spam, notifications only about new updates.

Related Posts