Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 34

 _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_



......Matsawa nayi baya ina kumbura fuska. “To ka buɗe min mana ba tana sashen Ummie ba. Oh Hajiya Babba”. Nai saurin gyarawa saboda kallon da naga ya wani kafeni da shi. Kamar bazai tanka min ba sai kuma a daƙile kamar an masa tilas ya ce, “Miya kaita can?”.

       “To ina ruwanka, kai dai ka matsa naje na ɗakko maka”.

     Shiru bai matsa ba ya dai zuba min ido kawai. Sai da ya mula dan kansa sannan ya sake furta, “Da gaske abinda Mammah ɗin ta faɗa kenan?”.

    Karon farko na ɗago na kallesa. Dan yanda yay maganar a dakensa ba ƙaramin tsargani yay ba. Idanuna cike da ƙwalla har muryata na rawa ma na ce, “Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”

        “Your are vary stupid!!”.

    Ya faɗa cikin katseni da daka tsawa. A take kuma idanunsa suka jirkice ƙwayar tsakkiya ta koma siririya, zaibar ta sake duhu exactly na maguna dai musamman idan suna a cikin hasken rana. Har cikin raina naji tsawar tashi ta ratsa ni, a take kwarjininsa da shakkarsa suka sake dabaibaye ni har na gagara sake magana. Sai da ya buɗe ƙofar a fusace ya fice sannan na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna. Lallai wannan mutumin yayi nisan da bai jin kira. Sannan akwai abinda ya kamata na sani dan na fahimci sam baya son abinda zai taɓa ahalinsa kenan. To lallai babbar magana. Dan ni inaji a jikina lallai akwai ɓoyayyen al'amari mai cike da darasi a ƙarƙashin ciwon mahaifiyar nan tasa. Amma in sha ALLAHU koma minene ni *_SAMRAAH ABDULL-WAHAB GWARZO_* nayi alƙawarin sai na bankaɗosa. Uban kowa sai ya kwashi kashinsa a tafin hannunasa cikin MAASH MANSION..

       (Tofa babbar magana. ALLAH ya bada nasara Kandala🥱). 


     Cikin cije baki da tabbatar da alwashina na nufi ƙofar nima. Dan nayi alƙawarin bazan sake bari mutumin nan yaga gazawata ba duk da ina jin shakkar tasa. Abincin rana dana tuna shine dalilin fitowata na ɗibama Ummie yasa hankalina tashi. Harna nufi hanyar barin sashen na fasa, dan sama-sama na ke jiyo magana ata falo. Falon na nufa, acan ɗin kuwa na samesa tare da ɗan kaɗafin PA ɗinsa. Yana zaune hannayensa duka dafe da kansa alamar akwai abinda ke damunsa ko kuma kan nasa na masa ciwo ne oho masa, PA ɗinsa tsaye ata gefensa cikin tsaiwar nuna girmamawa da alama magana yake masa. Ina fitowa yay shiru. Harara na watsa masa dai-dai muna haɗa ido. 

       “Barka da rana ranki ya daɗe”.

Ya faɗa dai-dai ina isowa inda suken. Wani ƙululun takaici ne naji ya shaƙuremin maƙoshi. Sai dai na danne na watsar da banza tamkar ma banjisa ba. Ledojin dana gani a gaban ogan nasa da bana raba ɗayan biyu abincine na ɗauka. Harna ɗauka ɗaya na sake tattaro sauran biyun ma na kwashe. Dai-dai na ɗago zan bar wajen PA ɗin nasa ya ce, “Ranki ya daɗe ɗaya ne extra, sauran na Boss ne”.

       “Ko zaka ƙwatar masa?”.

   Na faɗa a kausashe ina watsa masa wani shegen kallo. Da sauri ya girgiza kansa da faɗin, “A'a ayi haƙuri”.

     Tsaki naja mai ƙarfi, ina sake balla musu harara su duka biyun. Sai dai har yanzu kan ogan nasa na ƙasa bai ɗago ba, tamkar ma bai san mike faruwa a falon ba. Nima ba shine a gabana ba, dan haka nai gaba abina ina jan tsaki mai ƙarfi..


    ★Tana shigewa Hayatu dake kallon ogan nasa da tunanin zaice wani abu amma babu alamar hakan ya sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa da girmamawa ya ce, “Sir bari to na samo maka wani abincin tunda ta ɗauke wannan ɗin duka ko?”.

   Shiru kamar Maash ɗin bazai tanka ba. Dan har Hayatu ya fidda rai da samun amsa sai kuma ya ga ya ɗago ya kalla hanayar da tabi, ɗauke idanunsa yay ya maida ga Hayatun. Cikin yanayin nan nasa a daƙile ya furta. “Barshi kawai. Kaje ku ƙarasa abinda zakuyi. Ina sake gargaɗin ko su Juliet kar su san ina ƙasar nan yau.”

         “In sha ALLAHU zan kiyaye Sir. Amma idan mun tafi yau wazai dinga samo maka abinci? Ko dai nayi magana da gidan abincin kullum su dinga kawo order sau uku har cikar sati ɗayan”.

     Shiru kamar bazai ce komai ba. Sai kuma miya tuna oho. A hankali ya furta, “Kayi hakan”.

    Cikin jin daɗi Hayatu ya ce, “A huta kafiya”. Duk da yana mamakin ogan nasa akan daina cin abincin gidan a ɗan tsakanin nan bazai iya tambayar dalili ba. Dan tun washe garin birthday party ɗin Ummie ya sallami kukunsa dake masa girgiki, duk da ma dai ba ko yaushe bane yake cin abincin nasa yana cin na can cikin gidan a wasu lokutan musamman idan Aunty Mama na gari...


       💞⭐💞⭐💞


    Tunda suka idar da sallar kanta ke a ƙasa ta gagara ɗagowa ta kallesa. Yayinda shi kuma ya kafeta da idanunsa cike da nazari. Ganin yanda ta takure kanta waje ɗaya ya sashi ɗan sauke ajiyar zuciya. Kafin a hankali yay kiran sunanta..

      “Halimatussa'adiyya”.

   Da ƙyar ta iya ɗagowa tana amsa masa da, “Na'am”. Dai-dai suna haɗa ido. Saurin maida kanta tai ta sunkuyar. Murmushi ya saki da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya gyara yanayinsa cikin kame kai ya ce, “Wanene ni a wajenki?!”.

       Kasa cewa komai tayi, sai da ya sake maimaitawa. Muryarta na rawa tana sake sunkuyar da kai a hankali ta ce, “Baba!”.

      Murmushi yay mai faɗi tare da girgiza kansa. “Halimatussa'adiyya ni ba babanki bane. Mijinki ne ni, nasan kuma kin sani.”

         Kanta ta sake sunkuyarwa alamar dai ta san haka ɗin ne. Shima sai ya cigaba da faɗin, “Halimatu nasan ke mai tarbiyya ce da ilimin addini gwargwado. Dan naje har tushenki naga gidan da kika fito. Kema a karan kanki a ɗan zamanki cikinmu gidan nan na tabbatar da hakan. Fatana dai ALLAH yasa abinda na gani yasa ya ɗore har abada. Zuwa yanzu kema nasan kin san gidan da kika shigo. Kin kuma san wanda kika aura. Ni ba yaro bane ba, inada ƴaƴa biyu maza Musaddiq da Abbas da suka girme miki, inada ƴaƴa biyu mata Samraah da Sakina (Baby) da zaku iya sa'anni, inada waɗanda zaki iya girma Hafiz, Nabil, Habiba auta Jamal. Ina roƙonki dan ALLAH ki zauna lafiya da su, ki jasu jikinki matsayin uwa. Kada kiyi dubi da matsayin wadda suka girma ko kuke sa'anni. Mahaifiyarsu karki damu da abinda ke tsakanina da ita. Ki zauna da ita lafiya ki bata girmanta. Dan ALLAH duk wata hanya da zata zama ta raini a tsakaninku kada ki buɗeta. Ni kuma na miki alƙawarin in sha ALLAHU zan ƙare miki mutuncinki tako wane ɓangare. Nima na baki amanar kaina. Ki riƙeni da hannu biyu Please Halimatussa'adiyya. Dan ni da ke duk marayune”.

    Cike da mamakin jin kalmar Maraya daya kira kansa yadata ɗagowa ta kallesa.

        Cikin lumshe ido ya jinjina mata kansa. “Hakane Halimatu, nima maraya ne da babu uwa babu uba sai Gwaggo na kawai da ku da ALLAH ya bani matsayin iyali, sai ahalina na Gwarzo da sai a hankali zaki san kowa da kowa”.

      Kanta ta jinjina masa, sai kuma takai hannu ta share hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya saki tare da mika mata hannunsa na dama yana faɗin, “Zo nan”.    

      Da ƙyar ta iya motsawa zuwa gabansa, sai dai tabar ƴar tazara a tsakaninsu. Dan haka ya kamo hannayenta ya jawota sosai ya manna da jikinsa. Zata noƙe ya sake mannata da jikin nasa tare da zame hijjab ɗinta ya ajiye gefe. Ledar takeaway daya shigo da ita ya jawo gabansu. Ta gefen ido Halime take satar kallon dankareriyar kazar da ƙamshinta ya gama cika ɗakin. Yawu ta haɗiya zuciyarta na zallo, sai dai kunya ta hanata yin ƙwaƙwƙwaran motsi. 

       Cike da kulawa Abba ya ɗiba naman ya kai bakinta. Babu musu ko kwana-kwana ta amsa sai dai idanunta a rufe dan kunya. Shi dai Abba dariyama ta bashi, amma ya danne abarsa. Sai da Halime tai nak da naman kaji da yogurt sannan ta kauda kanta.......✍️


       🥱Gara da kikaci abinki Aunty Halime😂😜.


 



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 34"