Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 33

𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_



.......A bazata naji saukar muryarsa cikin kunnena. 

     “Ba abinda kika zo gani ba kenan?”. Ya faɗa a hankali cikin daƙilalliyar muryar nan tasa. Bamma san lokacin dana juyo a fusace na ce, “ALLAH ya kiyaye sai kace wata ƴar iska. Kuma ni ka bani hanya na wuce”.

       Maimakon bani hanyar ko tanka min sai ya shiga matso ni. Baya na farayi hankalina a tashe, idanuna na fitowa gaba ɗaya waje. Shi kuma bai fasa biyonin ba har sai da muka dangane da ƙaton gadonsa dake a dunƙule tamkar zero. Ganin baida alamar dakatawa na faɗa saman gadon idanuna cike da ƙwalla. Gaba ɗayansa ya ranƙwafo kaina yay min runfa hannayensa duka biyu dafe da gadon ta gefe da gefe na. Kaina na shiga girgiza masa idanuna cike da hawaye. Kafin na buɗe baki da ƙyar cikin ƙarfin hali na ce, “ALLAH zan maka ihun da kowa na gidan nan sai yazo sashen nan”.

        Wani lalataccen murmushi ya saki da ɗage gira ɗaya sama. A hankali ya sake matso da furkarsa gab da tawa. Ai babu shiri na ƙanƙame jikina tare da rumtse idanuna na kauda fuskata gefe. Amma duk da haka ina jin saukar dumin numfashinsa akan fuskar tawa. Kafin cikin maganar raɗa a cikin kunnena ya furta, “Da kuwa kowa a yau yasan ke ɗin *_MATAR AWWAB EL-MU'AZZ MAASH_* ce. Idan kuma kin cika matsiwaciya dan ALLAH ki gwada ki mana”.

       Hannu nasa na ture fuskarsa batare dana buɗe idanun ba, sai kuma na yunƙura zan tashi dan ji nake tamkar an sakani a kuttun man shanu tsabar yanda kusancinmu ya dabaibaye ni. Da sauri na koma ina mai dafe kaina daya bugu da nasa. Tare da buɗe idanuna ina ɓata fuska tamkar zanyi kuka. Shima tashi fuskar a yamutse take hannunsa dafe da goshinsa alamar yaji zafi, ban san sanda na bushe da dariya ba tsabar jin daɗi. Ganin yanda ya zuba min idanu ya sani haɗiye dariyar na ɓata fuska da harararsa na ɗauke kaina gefe. 

         “Baki da kunya ko?”.

     Ya faɗa cikin wani yanayi dana kasa fassarawa. Baki na sake murguɗawa fuskata a gefe a tunanina bai gani ba. Sai jinai ya furta, “Humm harara a duhu ai na mai tsoro ne. Idan kin isa kiyi ido cikin ido ni kuma zan banbance miki tsakanin aya da tsakkuwa. Bani phone ɗina”.

      Da sauri na juyo na kallesa danni nama manta da wani batun wayarsa a hannuna. Sai kuma na maida kaina gefe nace, “Ta ƙarfi ce. Kuma ni ka tashi min a kai, wannan ai rashin kun.....” na kasa ƙarasawa.

    Bai tashin ba bai kuma tanka min ba. Kusan tsahon mintuna biyu sai da ya mula dan kansa sannan ya miƙe kamar wanda akai ma ishara da hakan, dan da ƴar sassarfa ya bar wajen haƙoransa cije da lips ɗinsa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, har ina kai hannuna na fara ma kaina fifita da shi dan sam ko sanyin acn dake ɗakin baya wani ratsani. Jin rufe ƙofa ya sani zabura, sai naga bathroom ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sosai tare da miƙewa. Dan gwara nabar masa ɗakin kafin ya fito min a tsirara kuma tunda naga idanunsa ba kunyace a cikinsu ba. Turus na tsaya tamkar zan fasa ihu jin ƙofar a garƙame, a take naji sabon tashin hankali da hajijiya na neman kwasata, dan na fahimci ƙofar ya rufe kenan....


       ⭐💞⭐💞⭐


      Yanda take safa da marwa cikin ɗimuwa a ɗakin zai tabbatar maka da ranta a ɓace yake. Tabbas kuwa ran nata a ɓacen yake. Dan tunda take ba'a taɓa raina mata hankali irin na kwanakin nan ba. Musamman ma yau. Ranar Awwab ya gasa musu magana harda gorin gidan uwarsa ta tursasa kanta shanyewa batace komai ba saboda wani dalili. Yau kuma yarinya ƙarama tai mata rashin kunya da tsallake dokarta shi kuma ya mata tsawa ya kuma hana ta hukuntata. Kowa fa a gidan nan tsoronta yake ji, amma har yau a samu yarinyar da zata ƙaryatata a gaban ƴan aiki da ƴaƴanta. Lallai sai ta ajiye lesson mai ƙarfin gaske akan yarinyar nan. Kai hatta da Awwab bazata ƙyale ba saboda goyan bayan yarinyar ta fahimci yake yi. Ai ba yau ta fara cin uban ƴan aiki a gidan ba. Kuma ko yana zaune a wajen take yi ɗin ko ɗaga kai ya kalla baya yi ma. Amma ta kula akan yarinyar nan yana neman kawo musu wani sabon salo. Jiba randa Hajiya Babba ta daketa, ɗaukartafa ya dinga yi harda ɗorata a jikinsa yay treating nata da kansa. Kai ita fa gaba ɗaya ma kanta ya kulle. 

        Waya ta jawo tai kira. Ana ɗagawa ko sallama bata tsaya yi ba ta fara magana cikin damuwar dake tabbatar da ɓacin ranta. Abinda ya faru tun daga randa aka kawo Samraah gidan take sanarma wadda ta kira har zuwa yau ɗin nan. Sai kuma tai ɗan jimm alamar sauraren abinda na can ɓangaren ke cewa. Tsawon kusan mintuna uku kafin ta saki murmushi mai ƙayatarwa, tare da furta, “Kai amma na gode Hajiya Rubayya, Please kiyi maza ki shigo ina saurarenki. Dan wannan shawarar taki na fara jinta a jikina ƙwarai da gaske.” ajiye wayar tai tana sakin dariyar nasara. Sai kuma ta miƙe tamkar ba itaba ta fara zame kayan jikinta cike da nishaɗi. Tana kammalawa tiɓi-tiɓi ko kunyar kanta bata ji ba ta nufi bathroom ɗinta a haka da alama wanka zatayi.....


        💞💞💞💞


  *_INDIA_*


         Kuka take sosai da ƙoƙarin riƙe hannunsa daga haɗa kayan da yake tayi. Sai dai ko kallon inda take baiyi ba balle ya dakata da abinda yake ɗin. Cikin matsanancin takaici da fusata Attahir da ya gama harzuƙa da abinda ke faruwa ya fisge jakar yana mai dakama ƙanin nasa tsawa.

    “Mansoor are you mad ne wai?”.

           “Yes! I'm. Na ce I'm!. Ba haka kuke son ku ganni ba. Ko ba haka kukafi buƙatar ganina ba?. Nace muku ga wadda nake so, kun rabani da ita batare data ma wani cikinku laifin komai ba. Duk da abin yana min ciwo har yau har gobe ban taɓa ce muku komai ba. Amma hakan bai muku ba kuma sai ace min wai ga mata an ɗaura min aure da ita. Tunda nake da ku na taɓa ce muku ina son wannan yarinyar ne? Wlhy da nayi rayuwar aure da wannan yarinyar gara na shiga duniya. Na gaji da wannan rayuwar haka nan haba. Sai kace ba jininku bane ni, yaya kuke so na cigaba da rayuwa cikin salama ns wa....” kuka ya sarƙesa ya kasa cigaba da magana. Sai ma zubewa da yay a saman gadon yana mai dafe kansa dake sara masa da duka hannayensa biyu, tare da cusa hannunsa cikin sumarsa ya yamutsata.

       Sosai jikinsu ya sake yin sanyi. Musamman Mamy da tafi kowa kasancewa a cikin ɗimuwa. Itama zubewa tayi a gaban Mansoor ɗin tare da kamo hannayensa cikin nata tana sake fashewa da kuka. Dad ne da tun ɗazun baice komai ba ya furzar da iska mai kauri daga bakinsa, tare da kai hannu saman kansa ya shafo. Sosai kukan Mamy da Mansoor ke cizon zuciyarsa. Sai dai shi baima san ta inda zai fara ba game da wannan hargitsi daya rasa tushensa balle iyaka.....

       Kakarin da Mansoor ya fara ne ya maidosa a hayyacinsa. Kusan a tare shi da Attahir suka zabura kansa. Yayinda Mamy ta sake ɗimaucewa. Yunƙurin amai ya fara sai ga jini bula. Ihu Mamy ta fasa, yayinda Attahir ya fita a guje yana faɗin bari yay kiran asibiti...

       Kafin cikar mintuna goma ambulance ta iso. Lokacin da aka fito da Mansoor daga ɗakin hotel ɗin da suke ya gama fita a hayyacinsa. Dama yau kwana uku kenan da sallamosa baya kwanakin kusan wata guda daya kwashe yana jiyya. Samun lafiyar tasa ya saka walwala da farin cikin kowa dawowa a cikin ahalin nasa. Dan nan da kwanaki biyu ma suke shirin komawa gida Nigeria. Sai kuma aka samu akasi Husnah yarinyar Auntynsa da aka ɗaura masa aure da ita a randa aka fasa da Samraah dake Dubai ta ɓaro musu aiki tai kiransa a waya. Kalaman da tayi amfani da su a wajen gaisawar tasu ya sakashi neman fashin baƙi a wajen yayansa Attahir. Shi kuma batare da tunanin komai ba ya buɗe masa zancen cewar ai da gaske Husnah ɗin take an ɗaura mata aure da shi a randa aka fasa da Samraah. Wannan shine dalilin rikicin na yanzu, ga shi kuma da alama aiki ya koma baya.....    


      🌜🌟🌛


    Ina nan tsaye abin duniya duk ya isheni ya buɗe ƙofar bathroom ɗin alamar zai fito. Koda gigi ban yarda na kalla wajen ba balle ma na saka kaina a uku. Har tsawon mintuna uku ina ɗan jin motsinsa cikin yanayin rashin hayaniya. Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya na ce, “Ni ka buɗe min ƙofa na fita bana son taɓara”.

     Shiru babu alamar zai amsa min, daurewa nai na sake maimaitawa cike da tsiwa. Nan ma banji alamar zai kulani ɗin ba. Sai kawai na taune lips ɗina ina jin kamar naje na rufesa da duka. Tsahon mintuna goma ina dai wajen a tsaye ban juya ba ban kuma gusa ba. A bazata naji sautin muryarsa a bayana.

         “Bani phone ɗina”.

     Da sauri na juyo har ina buge hannu da ƙofa. A tsayen kuwa yake ƙyam a bayan nawa shantali guda dashi, dan duk nawa tsawon sai na ganni ɗis a gabansa. Ga fuskarsa a tsuke babu alamar wasa tattare da shi. Duk da yanda naji zuciyata ta motsa na tsorata sai na dake nima ina mai tsuke tawa fuskar tamau harda su hura hanci.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


 

Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 33"