Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 31

 _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_



.......Da sauri na jinjina mata kai ina ƙoƙarin miƙewa. “To Ummie in sha ALLAHU yanzu zan kawo miki abinci bani ɗan lokaci ƙalilan.” ban jira amsawarta ba na tashi na fita a guje dan nasan bama amsawar zatai ba. A falonta na farko naci karo da wasu mata guda uku sabbin fuska daban sani ba a gidan. Nayi mamaki dan ɗazun ban gansu ba, ko kuma ban lura dasu bane oho. Takan kowa banbi ba a cikinsu nafice zuwa downstairs na afka kitchen, ganin an gama komai har an gyara kitchen ɗin ma fito dining, komai an shirya na breakfast, sai dai babu kowa a kai dan sai sun gama barcin safensu suke fitowa karyawar. Hajiya Ƙarama ce kawai bata a gidan ta wuce wajen aiki. Komai sai da na ɗiba tare da haɗa shayi mai ƙauri na ɗauka ruwa. Da gudu na koma saman, inda na barta nan na sameta, sai dai yanzu tana kwance ta naɗe a waje guda sai nishi take alamar yunwar tacita ta cinye matan nan na tsaitsaye a kanta kamar a tsorace. Ina shigowa duk suka zabura kanta. Tsawa na daka musu tare da nuna musu ƙofa alamar su fita. Har rige-rigen fitar kuwa sukeyi. Basket ɗin hannuna na ajiye, sannan na durƙusa gabanta na ɗagota. A jikina na sanyata ina kuka da bata haƙuri, shayin dana haɗa dai-dai zafi na ɗauka na kai bakinta, jikinta har rawa yake wajen damƙe kofin, tsam ta dafesa tare da hannayena kamar mai lafiya, kwal-kwal ta shiga kwankwaɗar shayin tamkar ta samu ruwa. Kafin wani dogon lokaci ta shanyesa gaba ɗaya, sai ga zufa na karyo mata tako ina ta fara sauke ajiyar zuciya jikinta na saki. Jinai hawaye sun ƙara ziraro min, na kwantar da kanta sosai a saman cinyata ina shafa cuɗaɗɗen gashinta daya danƙare saboda datti. Tabbas ɗiya mace daban ce, da ace baiwar ALLAHr nan nada ƴa mace a cikin ƴaƴanta duk tsanani bazata dinga barinta a cikin wannan dattin ba. Amma kalla yanda aka saketa kamar mara gata. Dukiyar tatace, gidan ma nata ne, ɗan da suke taƙamar da shi a yanzu haka nata ne. Amma ita bata san daɗin ko ɗaya a ciki ba, sai wasu banzaye da sukazo suka cika gidan badan su amfana mata da komai ba. In sha ALLAHU na ɗauki alƙawarin daga yau koda baiwar ALLAHr nan zata halakani sai na ƙwato mata ƴancin rayuwarta a gidan nan, tun daga kula da ita har zuwa sanin tushen wannan ciwo nata da nake ji a raina ba banza ba. Kai harma ɗan nata da alama ba haka suka barsa ba shima. Sai da na tabbatar shayin da tasha ya faɗa mata sosai sannan na jawo abinci, ban tasheta a jikin nawa ba, a haka na dinga bata da kaina kuma tana amsa. Sai kallona take dan har ta kauda kanta alamar ta ƙoshi idonta a kaina ƙyam. Lemo na ɗakko zan bata ta kauda kai, sai na ajiye na ɗauki ruwa. Ina saka mata a baki kuwa ta hau sha. Sosai tasha tana sauke numfashi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikina, mintuna bai fi biyu ba barci mai nauyi ya dauketa. Ganin barcin nata yay nisa na fara kwance mata kitson kanta da yay bala'in danƙarewa, da naga ta motsa sai na ɗan dakata, sai ta koma barcin sai na cigaba. A haka na kwance gashin tana barci a jikina. Sosai take da gashi, da alama shima a wajenta ya gaji wannan gashin nashin da yakema mutane iyayi da shi. Ganin barcin nata yayi nisa na lallaɓa na kwantar da ita, gyaran sashen na fara, harda wancan ɗakin da naci duka a ciki wancan karon. Da yake na saka aikin a raina kuma an rage dattin da yay wancan karon sosai koma nace an gyara komai ƙal sai dai ban san wanda ya gyara ba kafin wani dogon lokaci na kammala tsaff, amma ina zargin matan nan dana gani sabbin ma'aikata ne aka kawo mata, maybe kuma sune sukai aikin. Ko'ina sai ƙamshi yake kamar ba shi ba, ruwa na haɗa inata tunanin ta yanda zatai wanka, dan harga ALLAH jikinta na buƙatar wanka, saboda alamu sun nuna an ɗan rage dattin jikinta ba kamar a ranar farko dana sameta na, harma kayan bana waccan ranar bane ba, sai dai kamar kuma ba'a sake mata ba tun waccan ranar ɗin. Ni kuma bamma san ta yanda zan iya cewa zan mata ba dan ina jin kunya. Dabara ce ta faɗo min, na fita zuwa kitchen dan nasan yanzu sun dawo aikin rana. Babu kowa a falon kuwa, cikin sa'a kuma na samu Mama Balki a dining tsaye tana waya. Tana ganina ta yanke kiran. Sai da ta wawwaiga ta tabbatar babu kowa a wajen sannan ta kama hannuna. Can ƙarƙashin stairs muka je, fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ina kika shiga Kandala? Tun ɗazun ake nemanki a gidan nan amma babu ke”.

    Kaina tsaye nace mata, “Mama ina sashen Hajiya Babba fa. Yanzu ma kiranki nazo yi ki taimakeni”.

      Sosai fuskarta ta nuna mamaki, ta ce, “Sashen Hajiya Babba fa?”.

    “Eh wlhy Mama. Dan ALLAH kizo ma muje kiga taimakon da zaki min kafin wani ya gammu anan a hanamu. Bata musa ba muka hau upstairs. Ni kaina tsaye nake tafiya, yayinda ita kuma take ta faman waige-waige da gani duk a tsarge take. Ita kanta sai da tayi mamakin yanda na ƙara gyara sashen, Hajiya Babba dake kwance na nuna mata. “Mama ki taimakeni jikinta na buƙatar wanka ne. Idan akai mata zataji sanyi. Ga kanta na buƙatar wanki ma, sannan matan can dake zaune a falon farko wai su wanene?”.

       Ɗan jimm tai alamar tunani, sai kuma ta amsa min da, “To yanzu yaya za'ayi kenan? Kin san fa dole aka saka mata ruwa a jiki dole ta farka. Kuma hakan akwai matsala shiyyasa ma Alhaji ƙarami ya hana a jika mata kai ranar. Waɗan can matan kuma sune sabbin masu aiki da Baba ya kawo tun ranar da abin can ya faru tsakaninku”.

     “Mama in sha ALLAHU baza'a samu matsala ba. Dan yanzu da kanta taci abinci. Kota farka kuma da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru mama. Su kuma ki gargaɗesu dan ALLAH ko kuma suje waje idan anjima sa dawo”.

    Badan ta gamsu ba ta yarda da magana ta, da taimakona muka kamata zuwa bathroom. Sannan ta fita ban san yaya tayi da matan ba ta dawo. Sake ɗaukar ta mukayi zuwa toilet. Ganin ta buɗe idanunta alamar ta farka cikin ruwan dana haɗa a bathtub muka sakata. Da farko taso zabura, sai da na dafe mata hannu da sauri cikin lallashi da roƙo ga hawaye a fuskata ina tofa mata addu'a sannan ta haƙura ta koma ta zauna. Kanta muka fara ƙoƙarin wankewa, sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Yanda wata muguwar dauɗa ke fita ban san lokacin dana ƙara ƙarfin kukana ba dan tausayi. Kai da kaga wannan baiwa kasan kafin lalurar na anyi manyan hamshaƙan mata. Amma jiba yanda ƙaddara ta maidata, ɗan adam kenan ba'a bakin komai yake ba. Bamu bar kan ba sai da ya koma fidda farar kumfa sol da ruwa mai ƙyau, baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take, barci ma ɗibarta yake. Fitowa nayi nabar Mama Balki tai mata wanka, duk da na fahimci ita tana komai a tsorace ne. Sai dai Alhamdullah ta daure ta mata wanka na gaske duk da ni na fito duba kaya kozan samu. Anan dai ɗakin da muke babu, sai da na duba ɗayan kusa da ita dake a kulle sai nayi sa'an samu, ashe ɗakin duk kayan sawarta ne da duk wani abun buƙata na gyaran jiki. Da alama tana ɓatawa ne shiyyasa ake rufesa abar key ɗin a jiki, sai dai kuma babu tabbacin ana mata amfani da su, dan da jikinta baiyi wannan masifar dattin ba ai. Komai da za'a iya buƙata na ɗauka harda towel sannan na koma inda suke. Har lokacin basu fito ba, dan haka na miƙama Mama Balki towel guda biyu, na ajiye duk abinda zasu buƙata na fita dan ta samu damar shiryata. Ina daga falo zaune kusan mintinan talatin sai ga Mama Balki ta fito tana sharar hawaye ga murmushi akan fuskarta. Zumbur na miƙe ina tambayarta ko lafiya. Maimakon amsa saita jawoni jikinta ta rungume tana mai fashewa da kuka mai ƙarfi da sanya min albarka. Ban iya kwace jikina ba har sai da tayi mai isarta ta ɗagoni dan kanta. Hawayen nima na share kafin na sake tambayarta abinda ke faruwa.

        “Babu abinda ya faru Kandala. Ke dai ALLAH yay miki albarka. Kin kwatanta abinda wani bai taɓaba a gidan nan. Ashe baiwar ALLAHr nan ba kowane lokaci bane take a yanayin da ake gudunta. Dama ƙyaƙyƙyawar mace ce mai ƙyawun siffa da cikar haiba amma ƙaddara ta maidata haka. Zo ki ganta Kandala zo kiga cikar zati da asalin kwarjinin manyan mata dan ALLAH”.

    Jiki na rawa nabi Mama Balki. Muna shiga ciki sai da na kusa faɗuwa dan mamakin abinda naci karo da shi. Lallai anan Awwab ya gado cikakken ƙyawu da asalin kwarjini. Hatta da idanun magen nan nasa irin nata ne. Bamma san lokacin dana ƙarasa gareta cikin sassarfa ba na durƙushe, hannayenta duka na kamo a cikin nawa na runtse, tamkar wadda ke cikin hankalinta sai ta sakar min wani guntun murmushi tare da lumshe idanunta a lokaci guda ta buɗe sai kuma ta sake maidasu ta lumshe. Bamma san lokacin da ƙaunar matar ya ƙara mamaye jini da ɓargona ba. Nai zaman dirshan a gabanta na cigaba da kallonta tamkar na samu television. Tsahon lokaci ina a haka har sai da mama Balki ta fargar dani muyi mu fita kafin mutanen gidan su farga da zamanmu a ashen. Gashi su kansu wadancan matan bamu san a ƙarƙashin ikon wa suke ba. Kaina tsaye nace “To mama minene dan sun san muna anan? Dama ba so suke su sami mai kulawa da ita ba? Nifa waɗan nan matan bazasu cigaba da zama da ita ba sai dai su koma inda suka fito”.

     “Hummm” kawai Mama Balki tace dani batare da fashin baƙi ba. Daga haka ta fita tana mai tabbatar min nayi sauri na kammala tunda tayi barci na fito ita zata koma akan bakin aikinta. Da to kawai na amsa mata badan zanyi yanda tace ɗin ba, dan tana fitar ma kayan gyaran gashi na jawo tare da gyara zama na hau gyara gashin Ummie. Gashine mai uban yawa ga tsayi shiyyasa nasha wahala sosai. Ban bar mata shi a haka ba nai zaman kitsa mata shi. Nan ɗin ma dai ansha cakwakiya kafin a kammala, dan takan farka ta dafe hannuna tana yamutsa fuska. Har sai na tsaya ta huta ina tofa mata addu'a sannan nake cigaba. Sanda muka gama barcinta yayi nisa sosai, dan haka na miƙe na tattare kayan dana kawo mata abinci ɗazun da wanda nai gyaran gashinta na maida inda suke na fita da sauran samo mata wani abincin. Kusan cin karo mukai da yarinyar da Bahijja tace min agola ce a gidan, tana ƙoƙarin hawowa upstairs ina ƙoƙarin sauka ni kuma. A ɗan yamutse da kallon raini tace min nazo ana nemana........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 31"