Tsutsar Nama Book 2 page 29
?𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_
______________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
___________
.......Ba Mom kawai ba hatta ƙawayen nata sumar tsaye duk sukayi. Sai da suka sake jinfa tabbas a cikin gidanne sannan suka fara rige-rigen fitowa. Tamkar Mom zata tashi sama tai dirar mikiya a gaban wanda ke riƙe da amarya Halime. Cikin huci da fara birkicewa ta furta, “Kai lafiya? Daga ina haka? Su wanene ku?”.
Murmushi Hajiya Asabe uwargidan mai anguwa ta saki. Cikin dattako da cikar kamala ta bata amsa da, “Baƙi ne na alkairi da ga jihar Katsinan dikko ɗakin kara, kunya garemu tsoro babu”.
Duk da har cikin rai Mom taji shakkar matar, dan duk da mazauniyar ƙauye ce irin matan nan ne da aji a cikin jikinsu yake. Duk da dama can ita ba haihuwa da girman ƴan tumakin bace aurene ya kaita ƴar asalin cikin birnin Katsina ce. “Ke matsayinku ya dama, ni ba wannan ne matsalata ba. Wannan abar da aka lulluɓo nake son sanin matsayinta da dalilin shigowarku gidana”. Tai maganar tana nuna Halime da ke lulluɓe lafe a jikin Innarta Suwaiba. Duk abinda Mom ɗin keyi kuma tana jinta. Dan murmushi ma take yi ta cikin gyalen.
Kai tsaye Hajiya Asabe ta sake bama Mom ɗin amsa da, “Wannan ba huruminmu bane ba, inaga mijinki ne ya cancanci baki amsar kamar”. Daga haka ta sake jan hannun Halime zasu wuce. Idon Mom ya fara rufewa kuwa. Tana shirin sake magana Gwaggo Gudidi ta iso wajen, dama tana sallane shiyyasa bata fito a ƴan tarbar amaryar ba. Ko kallon inda Mom take batai ba ta shiga yima baƙi lalale marhaban, tare da isa inda Halime take ta kama hannunta tana faɗin, “Sannu da zuwa ɗiyata sannu kinji ƴar albarka”.
Yunƙurawa Mom ta sake yi a fusace zatayi magana wata maƙociyarta ta riƙeta. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Maman Baby kwantar da hankalinki, inagafa mutanen nan so suke kawai suyi yawo da hankalinki. Anya ba matar ɗanku bace Musaddiq”.
Da dauri Mom ta dubeta da idanunta da sukai jazur, cikin ɓacin rai da tashin hankalin daya gagara ɓoyuwa gareta ta ce, “Maman Nana Musaddiq kuma? Shine dan Musaddiq zaiyi aure sai a munafunceni? Sannan tayaya ma shi Imam zaiyi gangancin kawo min matar Musaddiq mu rayu a gida ɗaya. Kenan ma su ƴaƴana sun rako na wasu ne duniya”.
Ɗan jimm Maman Nana tayi, sai kuma ta jinjina kanta cike da gamsuwa. “To amma Maman Baby idan fa har ba hakan bane to tabbas Abban Abbas ne yayo aure batare da kin sani b....”
Wata muguwar ashariya Mom ta lailayima Maman Nana tare da wanke fuskarta da mari. Tuni hankalin kowa ya fara dawowa kansu. Dan kafin Mom ta sauke hannunta itama Maman Nana ta sauke mata marin. Su kam dangin amarya tuni sun gama shigewa cikin ɗaki da amaryarsu batare da sunbi takan hayaniyar data kaure tsakanin Mom ɗin da Maman Nana ba. Zaburar Mom da nufar sashen amaryar ya saka Gwaggo Gudidi cimmata ta tare ƙofar. Ƙoƙarin tureta Mom keyi cike da raini Aunty Na'ima ta janyeta rai ɓace. “Wai ke Jalilah miyasa baki da isashiyar tarbiyya ne? Ke yanzu sai ki ture Gwaggon kike nufi?”.
“Yo mizai hana nayi hakan, ai ni idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba, nima bazan ji kunyar kado shi ƙasa ba kuwa wlhy.”
“K Jalilah ki shiga hankalinki wlhy dan yanzu ba da bace. Kin kuma san ko ada ɗin ma ana ƙyaleki ne darajar wanda ya kwasoki cikinmu amma badan ana jin tsoronki ba. Hauka kuma dama kin saita kanki kafin ɗan sauran mutuncinki daya rage ya ƙarasa zubewa. Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys”.
Cak numfashin Mom ya tsaya tare da harbawar zuciyarta. (Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys) kalaman suka shiga maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarta cikin amsa kuwwa. A hankali ta ɗago tana kallon Aunty Ni'ima, sai kawai idanunta suka sauka akan Abba daya shigo. Rawa jikinta ya farayi, cikin ɗimuwa da sassarfa ta nufesa. Cak ya tsaya yana kallonta harta ƙaraso inda yaken. Yanda ta cakumo hannunsa zai tabbatar maka da bata a cikin hayyacinta, dan harshenta har sarƙewa yake wajen faɗin, “Abban Abbas wacece wannan aka kawo min gida? Matar wacece? Dan ALLAH kace min Abbas kaima aure”.
A hankali ya girgiza mata kansa tare da riƙo hannunta. “Jalilah Please relax mana..”
“Naƙi nayi relax ɗin Imamu ka faɗa min wacece ita?”.
“Zan faɗa miki amma ki muje daga ciki”.
“Wlhy babu inda zanje sai ka faɗa min anan. Kuma kaima ɗin baka isa kabar wajen nan ba....”
Gwaggo Gudidi ce ta ƙaraso wajen. Idonta akan Abba ta ce, “Miye kake wani zazzame mata Imamu, ka fito fili ka faɗa matan tunda ita ta nema da kanta. Ai shiyyasa ake son mace ta zama matar ƙwarai kodan irin wannan ranar. Idan ka zama ɗan arziƙi mai tarbiyya taya har miji zai ɗakko maka abokiyar zama batare da saninka ba. Ai dama halinka sabulun wankanka. Mata dai taka ce muma duk mun shaida. Hargowarta ko shirmenta bai isa sakawa a goge hakan ba. Dan in har kai gigin sakin wannan baiwar ALLAHr daka auro koda bayan raina ne wlhy kaf mu ahalinka bazamu yafe maka ba. Ballema nasan bazaka fara kwatanta hakan ba dan kaima kana ƙaunar matarka. Dan haka ka fito ka sanar mata aure ka ƙara dan bazaka cigaba da zama daga kai sai ita a cikin gida ba ta kasheka watarana kamar yanda ta rabaka da duk danginka damu iyayenk.....”
Babu wanda ya san ta yanda akai kawai hannun Mom aka gani a wuyan Abba ta cakumosa. So take tayi magana amma hakan ya gagara saboda numfashinta ma fisga yake. A mamakin kowa sai gani sukai tayi baya gaba ɗayanta alamar suma. Ƙasa take neman zubewa sai da Abban ya riƙota.....
🌜🥱🌛
Tunda tabar falon bai iya ya motsa daga inda yake zaune ba. Sai ma tsurama ƙofar da tabi idanunsa yay tamkar tana a wajen har yanzu. Yana nan zaune kusan mintuna goma shigowar Hayatu ta katse tunanin nasa. Koda Hayatun ya gaisheshi ma hannu kawai ya ɗaga masa. Shi dai Hayatu ya riga ya saba shiyyasa bai damu ba. Sai ma kaiwa da yay zaune bayan yaje gabansa ya ajiye takardun dake a hannunsa dan yau shi bai fita office ba sakamakon yini da sukai akan Hajiya Babba da likitocinta, tare da tsaftar sashenta aka fidda duk kayan da Samraah ta tattara dama sauran duk na sashen aka canja mata katifa kafin a kawo wasu. Shiyyasa Hayatun ya kawo masa duk wani document mai muhimmanci da zai duba ya saka hannu...
Ina fita na saki murmushin farin ciki. Yau dai na samu wayar yin magana da ƴan uwana. Duk da ko a da da nayi niyya zanyi hakan dan su Bahijja duk akwai waya a hannunsu. Abinda yasa ban taɓa ara ba saboda bana buƙatar kowa yasan sirrina. Farin cikin waya ya mantar dani wani batun aikin Hajiya Mammah. Dan amaimakon kitchen daya kamata na koma ficewata nayi daga sashen baki ɗaya ko su Azizat dake zaune acan rukunin ƙarshe na kujeru bana tunanin sun ma ganni. Ban nufi sashen mu ba na wuce garden ɗin gidan. Tsabar wuce wuri kuma maimakon babban garden sai na shige ƙaramin da akace nasa dan na samesa a buɗe da'alama aikin gyarashi akayi saboda kayan aiki dana gani an tule. Can na shige kusan ƙarshe duk dan dai na samu wajen ɓuya nai wayar a tsanake. Kaina tsaye na sake danna kiran layin Yaya Musaddiq. Sai dai harta katse bai ɗaga ba sai da na sake kira na biyu. Hayaniyar da naji ya sani faɗin, “Yaya ya nake jin hayaniya ko kana kasuwa ne?”.
Maimakon amsa ƴar dariya yayi da cewa, “Har kin gama darun?”.
“Kai Yaya ni har wani daru ne da ni?”.
“Sosai kuwa Kandalata. Ai ke naki ma na musamman ne.”
Karon farko na saki dariya, sai kuma na shiga gaishesa da girmamawa. Ya amsa min da kulawa tare da tambayar lafiyata da kuma jiyyar da nayi. Na amsa masa da Alhamdullah, tare da tambayarsa mi ake a gidan naji hayaniya. Kansa tsaye ya ce, “Mamarki akema kishiya”.
Da mamaki nace, “Mamata kuma Yaya? Wa kenan?”.
“Mom mana. Abba ne ya ƙara aure”.
Tuni na miƙe daga zaunen da nake dan mamaki, sai kuma na shiga ƙyalƙyala dariya. “Wai dan ALLAH yaya da gaske kake ko wasa? Mom fa akaima kishiya? Ta yaya Abba ya samu wannan ƙwarin gwiwar haka? A ina kuma ya samo matar?”.
Tsaf Yaya Musaddiq ya kwashe labari ya bani, tun daga zuwan Halime gidan har kawo yau da suke jiran isowar amarya batare da Mom ta sani ba. Tsabar farin ciki bamma san lokacin dana rangaɗa ghuɗa ba. Sai da Yaya yace min, “Ƙaniyarki kandala” sannan na bari ina dariya. Haka kawai nake jin raina fes da wannan al'amari. Dai-dai nan sautin muryar aunty Zakiyya data rangaɗa sallama ya ratsa kunnuwana. Bayan sun gama magana da Yaya Musaddiq yake cemata gani a waya. Amsa tayi cike da zumuɗi muka gaisa, kafin cikin raunin murya da lallashi ta ce, “Samraah shike nan kuma babu kira duk kinsa hankalinmu ya kasa kwanciya?”.
Murmushi nayi hawaye na cika min ido. Muryata na rawa na ce, “Aunty bani da waya ne. Kuma kuma kun sallamani ga wanda ban ko sani ba kamar bani da kowa a duniya”.
“Haba Samraah, shin bazamu iya haƙuri da karɓar ƙaddara ba a duk lokacin da tazo mana? A maimakon tada hankali a ganina godiya ya kamata muyima UBANGIJI dan a maimakon tozarcin da akaso ganinmu a ciki alkairi ne ke lulluɓe da mutuncin mu. Samraah kiyi haƙuri dan ALLAH, ki karɓa da hannu biyu sai ALLAH ya sauƙaƙa komai a yanda ba kowa yay zato ba. A kowace daƙiƙa ta rayuwa kuma kina ranmu. Kawai dan bamu san ta yanda zamu sameki bane ba”.
Babu daɗi kalamanta suke sake saka ni. Dan haka na sake raunana murya, “Aunty kina nufin maganar da wannan mutumin ya faɗa da Yaya gaskiya ce? Da shi aka ɗaura min aure, kuma aka kawo ni garesa? Shike nan kuma kun barmasa ni?”.
Ƴar dariya tayi, cikin wasa ta ce,.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 29"